Kotu ta saki shugaban ’yan ta’adda, Nnamdi Kanu

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Kotun ɗaukaka Ƙara ta Tarayyar Nijeriya da ke zamanta a Abuja ta ba da umarnin sakin shugaban ƙungiyar nan ta a ’yan ta’adda, wato IPOB, Nnamdi Kanu, ƙungiyar da a baya wata kotu ta tava ayyana a matsayin ta ’yan ta’adda.

A ranar Alhamis Kotun Ɗaukaka Ƙarar ta wanke Nnamdi Kanu daga laifin da Gwamantin Nijeriya ke zargin sa aikatawa na tayar da zauna tsaye da ta’addanci da kuma jagorantar haramtacciyar ƙungiya.

Lauyansa, Ifeanyi Ejiofor, ya sanar ta shafinsa na Facebook cewa, “Mun yi nasara, Kotun Ɗaukaka Ƙara ta wanke ta kuma saki Nnamdi Kani.”

A ranar 23 ga Disamba, 2015, aka fara gurfanar da shi a gaban kotu, kafin daga bisani kotun ta bayar da belinsa a ranar 25 ga Afrilu, 2017.

Daga baya ya saba sharaɗin belin nasa, ya ƙi zuwa halartar zaman kotun, inda ya arce daga ƙasar, amma daga baya jami’an tsaro suka taso ƙeyarsa daga ƙasar waje.

A lokacin da ya ke zaune a ƙasar waje, gwamnati ta zarge shi da tunzura mutane a Nijeriya su ɗauki doka a hannunsu, duk da cewa, kotun ƙasar ta ayyana neman shi ruwa a jallo.

Daga bisani jami’an tsaron Nijeriya suka yi gagarumar nasarar damƙe shi a wata ƙasa da ke nahiyar Afrika bayan da aka yi zargin cewa, sun haɗa baki da wasu wajen lasa masa zuma a baki kan ya zo nahiyar, don ba shi tallafin maƙudan kuxi, waɗanda zai yi amfani da su wajen cigaba da ayyukan yaɗa manufarsa a yankin Kudu Maso gabas na Nijeriya, inda yake jan hankalin mabiyansa masu fafutukar ɓallewa daga Nijeriya, don kafa ƙasar Biyafara.

By Editor