Daga CMG HAUSA
Kwanan nan kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta ƙasar Sin, ya kira wani taro na mutanen da ba ‘yan jam’iyyar ba ne a birnin Beijing, inda aka saurari ra’ayoyi, da shawarwari daga wajensu, kan daftarin tattaro ra’ayoyi, na rahoton babban taro karo na 20 na jam’iyyar.
Babban sakataren kwamitin ƙolin jam’iyyar kwaminis ta ƙasar Sin, Xi Jinping ne ya jagoranci taron, inda ya gabatar da wani muhimmin jawabi dake jaddada cewa, a sabon zamanin da muke ciki, kuma bisa sabbin buƙatu, ya dace jam’iyyar kwaminis da sauran wasu jam’iyyun ƙasar su ƙara haɗin-kai, don haɓaka nuna kishin ƙasa, da tattaro hikimomi da ƙarfi daga kowane ɓangare.
Da ƙarfafa gwiwar dukkanin al’ummun ƙasar, a wani ƙoƙari na ci gaba da raya ƙasar Sin ta zamani dake bin tsarin gurguzu daga dukkan fannoni, da farfaɗo da al’ummar ƙasar Sin baki ɗaya.
Mai fassara: Murtala Zhang
