Daga BASHIR ISAH
Ƙungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) ta janye yajin aikinta don bai wa mambobinta damar komawa bakin aiki.
Duk da dai kungiyar ba ta ba da sanarwar hakan a hukumance ba, amma jaridar Punch ta tattaro cewar an cimma matsayar janye yajin aikin ne bayan tattaunawar da shugabannin ƙungiyar na ƙasa suka yi a Abuja.
Majiyar Punch ta tabbatar cewa, ‘Lallai an janye yakin aikin.”
Sai dai majiyar ta ce a saurari shigaban ASUU na ƙasa domin ƙarin bayani da safiyar Juma’a.
Da alama dai ƙungiyar ta janye yajin aikin ne domin biyayya ga umarnin Kotun Ɗaukaka Ƙara inda ta buƙa i malamai su koma baki aiki.
Idan dai ba a manta ba, Manhaja ta rawaito ASUU ta soma yajin aikin nata ne ran 14 ga Fabrairun 2022, wato kimanin watanni takwas da suka gabata da zummar neman haƙƙoƙinta a wajen gwamnati.
