Sanata Hanga bai da hannu a dakatar da kacici-kacicin da  A.A. Zaura ke daukar nauyi – Nura Mai-ƙarfi

Spread the love

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano

An bayyana cewa Sanatan Kano ta Tsakiya Sanata Rufa’i  Sani Hanga ba shi da alaƙa da hana wani shiri na kacici-kacici da A.A. Zaura ya ɗauki nauyi ake gabatarwa a wani gidan rediyo.

Hon Nura Mai-ƙarfi Dala, Hadimi na musamman ga Sanatan ne ya bayyana hakan.

Ya yi nuni da cewa shi Sanata ba Gwamnati ba ne, baya hukunci don shi ba  kotu ba ne. Sanata ne da al’ummar Kano ta Tsakiya suka duba cancantarsa suka zaɓe shi yake musu wakilci a majalisar dattijai.

Hon. Nura Mai-ƙarfi ya ce maganar dakatar da kacici-kacici da muƙarraban A.A. Zaura suke, batu ne na kotu kuma Sanata Hanga bai kai ƙarar shirin kacici-kacici kotu ba ya kai ƙarar   wanda yake ɓata masa suna ne a shirin, maganar dakatar da shirin ko wani abu wannan magana ce a gaban kotu.

Ya yi nuni da cewa suna mutuƙar godiya ga irin gudunmawa da A. A Zaura yake bai wa al’umma. Sai dai ya  shawarce shi da cewa idan ya yi  duba da Jihar Kano akwai limamai da dagatai da masu unguwanni da ‘yan Hisba mutanen kirki, yana ganin idan rabon za a yi ga al’umma idan aka bi ta hannunsu saƙo zai isa ga al’umma.

Ya yi nuni da cewa akwai talakawa da ba su da waya, wasu ba su da kuɗin katin waya ma da za su sa suyi kira idan ana shirin kacici-kacicin. Wasu ma ba su da inda za su je su ji shirin a rediyo, sannan masu wayar ma ba lallai ne idan sun buga ma ba su samu ba, ko sun samu ba lallai su yi nasarar amsa tambaya da aka yi ba, alhali suna da buƙatar taimako.

Nura ya ce amma idan aka bi ta wancan tsarin na bai wa limamai, dagatai sa masu unguwanni  da yardar Allah za a yi nasara.

Hon. Nura Mai-ƙarfi Dala ya ce kamar su a  tafiyar su ta tsarin kwankwasiyya kowa ya sani harka ce ta jinƙai da tausasawa al’umma,wannan tsarin na ciyarwa a kansa suke, domin a baya ma kowace ƙaramar hukuma an kai buhu 450 na abinci kuma cikin yardar Allah za a cigaba.

Babban Hadimin na musamman ga  Sanatan Kano ta tsakiya.Nura Me ƙarfi Dala ya ce amma idan akace a shirin kacici-kacici da ake a mako za a yi sau ɗaya, idan an buga waya sai an yi sa’a mutum huɗu ko uku ne za su samu.

By ukarofi