Daga RABIU SANUSI a Kano
Shugaban Jam’iyyar SDP na Jihar Kano kuma sakataren Gamayyar Haɗakar Jam’iyyu, Hon. Ali Shettima Tudun Murtala ya bayyana cewa shirye-shiryen jam’iyyarsu ya yi nisa wajen batun tunkarar zaɓen ƙananan hukumomi da za a gudanar a jihar Kano.
Hon. Ali Tudun Murtala ya bayyana haka ne a wata zantawa da wakilan jaridu da ya yi a daidai lokacin da yake wa wakilan gidajen jaridu ƙarin haske kan shirin Jam’iyyar SDP.
Shugaban Jam’iyyar SDPn ya ce a yanayin da ake ciki yanzu yana da tabbacin jama’a ne za su zama alƙalai bisa irin yadda al’umma suke cikin halin matsin rayuwa.
Hon Ali wanda kuma shine sakataren tsare-tsaren gamayyar jam’iyyu a jihar Kano ya ce ba ƙaramin alkhairi ba ne gare su bisa bada umarnin gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi a fadin ƙasar nan.
“Ba mu da abinda za mu iya cewa a halin yanzu da ya wuce shugaban Hukumar zaɓe na jihar Kano ya yi adalci lokacin gudanar da wannan zaɓe.”
Shugaban na SDP ya kuma ce idan shugaban zaɓe Farfesa Malumfashi ya tsaya ya yi nazari zai ga babu abinda al’umma suke buƙata da ya wuce shugaban da suka zaba ba abinda wani ɓangare yake buƙata.
“Batun shiri na tunkarar zaɓe muna nan muna shiri, don haka ba za mu ba abokan hamayya satar amsa ba, amma muna shiri kuma akwai nasara in sha Allahu.
“Mun san shi Baturen zaɓe na wannan. Jihar tamu mutum ne wanda yasan abinda yake yi don haka ba mu da matsala kamar yadda muka yi magana da shi a wani taron shugabannin jam’iyyu da muka yi ƙasa da kwana biyu ya bayyana mana ƙudurinsa na gudabar da sahihin zaɓe, muna da kyakkyawar fahimta tare da sa ran zai kamanta adalci.”
