Sarkin Musulmi ya naɗa jikan Sardauna sarautar Magajin Garin Sakkwato

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Mai Alfarma Sarkin Musulmi kuma Shugaban Majalisar ƙoli ta Harkokin Addinin Musulunci ta Nijeriya (NSCIA), Alhaji Sa’ad Abubakar III, ya naɗa matashin ɗan shekara 23, Alhaji Ahmadu Bello Danbaba, a matsayin sabon Magajin Garin Sakkwato. Sabon Magajin Garin ya gaji mahaifinsa marigayi Alhaji Bello ɗanbaba, wanda shi ma jikan marigayi Firaministan Arewacin Nijeriya, Alhaji Sir Ahmadu Bello ne.

Haka kuma, marigayi Bello ɗanbaba ya fito ne daga zuriyar Alhaji Marafa ɗanbaba da Hajiya A’ishatu Ahmadu Bello, babbar ’yar Sardauna.

Sarautar Magajin Garin Sakkwato na daga cikin manyan muƙamai masu daraja a Fadar Sarkin Musulmi, kuma tana cikin Majalisar Sarauta ta Sakkwato a matsayin babban mashawarci.

Naɗin Ahmadu Bello Danbaba ya samu amincewar Gwamnan Jihar Sakkwato, Ahmed Aliyu, tare da wasu sababbin masu sarauta kimanin 20 da Sarkin Musulmi ya naɗa a fadarsa da ke Sakkwato.

A jawabinsa, Sarkin Musulmi ya hori sabbin masu sarautar da su kasance masu tsaka-tsaki a harkokin siyasa, su kuma zama uba ga kowa ba tare da nuna bambanci ba. Ya bayyana cewa wannan dama da suka samu na shugabanci wata baiwa ce daga Allah, don haka ya kamata su gudanar da ayyukansu cikin gaskiya, riƙon amana da sadaukarwa.

Ya kuma jaddada cewa shugabanci na buƙatar ƙwazo da jajircewa, tare da yin aiki domin ci gaban al’umma, yana mai kira gare su da su cika burin jama’ar da aka ɗora musu.

Daga cikin waɗanda aka naɗa akwai Alhaji Ibrahim Isa a matsayin Hakimin Gatawa, wanda shi ne ɗan marigayi Sarkin Kudun Gatawa, Alhaji Muhammad Bawa, wanda ya rasu a hannun ’yan bindiga. Sauran sun haɗa da Alhaji Ibrahim Muhammad Sanyinna a matsayin Ardon Sanyinna, Aminu Buhari Galadima a matsayin Sarkin Gabas Durbawa, da Alhaji Abdullahi Saidu Sifawa a matsayin Sarkin Kudun Sifawa.

Haka kuma an naɗa Aminu Ubandoma Abdullahi a matsayin Ubandoman Garin Hamma’ali, Alhaji Muhammadu Mode Guiwa a matsayin Sarkin Kudun Guiwa, Abubakar Umar Dogondaji a matsayin Sarkin Yamma Dogondaji, da Abdulrahman Yarin Gandi a matsayin Yarin Gandi, tare da wasu da dama.

A wajen bikin, Sakataren Gwamnatin Jihar Sakkwato, Alhaji Bello Sifawa, ya wakilci gwamnan jihar, yayin da Kwamishinan ƙananan Hukumomi da Harkokin Sarauta, Dakta Daddi Adare, da Shugaban Ma’aikatan Fadar Gwamnati, Abdullahi Dikko, suka halarta tare da sauran manyan baki.

Wannan naɗi na nuni da yadda ake ci gaba da ɗaga martabar tsarin sarauta a Arewacin Nijeriya, tare da haɗa sabbin jini cikin shugabanci domin ɗorewar al’adu da ci gaban al’umma.

By ukarofi