Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Shugaban ƙasar Amurka, Donald Trump, ya bayyana cewa yana da sha’awar “karɓe man fetur na ƙasar Iran,” tare da yiwuwar mamaye tsibirin Kharg, duk da cewa a lokaci guda yana jaddada cewa tattaunawar da ake yi da Tehran na tafiya yadda ya kamata, kuma yana da tabbacin za a cimma yarjejeniyar zaman lafiya nan ba da jimawa ba.
Trump ya bayyana wannan ra’ayi ne a wata hira da aka wallafa a jaridar Financial Times a ranar 29 ga Maris, sannan ya sake yin ƙarin bayani ga ‘yan jarida a cikin jirgin shugaban ƙasa na Air Force One.
A cewarsa, ana samun ci gaba a tattaunawar da ake yi da Iran, inda ya bayyana cewa ana gudanar da ita kai tsaye da kuma ta hanyar ɓangare na uku tare da shugabannin da ya kira “masu hankali.” Ya kuma yi iƙirarin cewa Tehran na sassauta matakan buɗe mashigar ruwa ta Hormuz, wacce ke da matuƙar muhimmanci domin kusan kashi 20 cikin ɗari na man fetur da iskar gas na duniya na ratsa ta.
Sai dai bai yi ƙarin haske kan abin da ya kira tattaunawa kai tsaye da Iran ba, yayin da mahukuntan Tehran ke musanta cewa akwai irin wannan tattaunawa. A cewar Iran, ta karɓi wata shirin zaman lafiya mai maki 15 daga Amurka ta hannun jakadu daga Pakistan, amma ta yi watsi da shi bayan nazari.
Trump ya ce, “Muna tafiya da kyau a tattaunawar, amma ba za ka taɓa sanin yadda Iran za ta kasance ba. Muna tattaunawa da su, amma wani lokaci sai mu kai musu hari… ko da ta hanyar jiragen yaƙi irin su B-52, ko kuma ta hanyar soke yarjejeniyar nukiliya ta 2015 da suka rattaba hannu a kanta tare da manyan ƙasashe kamar Amurka, Rasha da China.”
Ya ƙara da cewa, yana ganin za a iya cimma yarjejeniya da Iran, amma bai cire yiwuwar rashin nasara ba. A wani ɓangare kuma, ya yi iƙirarin cewa tsarin mulkin Iran ya riga ya rushe, duk da cewa bai gabatar da hujjoji dalla-dalla ba.
A hirarsa da Financial Times, Trump ya jaddada cewa zai fi son karɓe man fetur na Iran, yana kwatanta hakan da abin da ya faru a ɓenezuela, inda ya ce Amurka na shirin ci gaba da rike masana’antar man fetur na ƙasar na tsawon lokaci bayan kama shugabanta, Nicolas Maduro.
Ya ce, “A gaskiya, abin da na fi so shi ne mu karɓe man Iran, amma wasu mutane a Amurka suna tambaya me ya sa, alhali ba su fahimta ba.”
Dangane da tsibirin Kharg, Trump ya ce Amurka na da zaɓuɓɓuka da dama, yana mai cewa, “Wataƙila mu karɓe shi, wataƙila kuma ba za mu yi haka ba.” Tsibirin na da matuƙar muhimmanci domin shi ne cibiyar da ake fitar da mafi yawan man fetur na Iran zuwa kasuwannin duniya.
Wannan matsayi na Trump ya sake tayar da muhawara a duniya, musamman kan yadda yake haɗa barazana da kuma magana kan zaman lafiya a lokaci guda, lamarin da ke ƙara jefa shakku kan makomar dangantakar Amurka da Iran.
