Shehu Saulawa: Rai baƙon duniya

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA

Ta ina zan fara wannan rubutu da na so yi tun lokacin zafin babban zaɓen Nijeriya na shugaban ƙasa da ’yan majalisar dokoki a ranar 25 ga watan jiya. Mu na cikin ɗakin sauraron sakamakon zaɓe a lokacin da a ka kawo sanarwar farko ta sakamakon jihar Ekiti ne in zan tuna daidai sai Saleh Shehu Ashaka ya bugo min waya bayan mun ɗan yi taƙaitacciyar magana sai ya ce min “ka na da labarin rasuwar Shehu Saulawa?” nan fa na ɗauka da Inaa Lillahi Wa Inna Ilaihi Raji’un, Allah ya yi wa Saulawa rasuwa?

Rayuwa kenan duk mai rai wataran mamaci ne. Haka a ka zo daya bayan daya nan duniya kuma haka za a koma ɗaya bayan ɗayan ko ma gaiya a lokaci ɗaya duk nufin mahaliccin sammai da ƙassai ne. Abun addu’a har kullum mu samu cikawa da Imani kuma kar mu bar baya da ƙura.

Tun ma shigar mu dakin bayyana sakamakon a babban ɗakin taro na ƙasa da ƙasa da ke Abuja mai suna ICC a takaice mu ka yi juyayin rasuwar dan jarida kuma wakilin rediyon Faransa Aminu Manu wanda da shi mu ka ɗauki labarun sakamakon zaɓen 2019 a wannan ɗakin taron.

Mu ka duba ashe ba zai samu dawowa don ba da rahotannin zaven 2023 ba. Mu ka ga mu kuma da Allah ya hukunta mun samu dawowa ba lalle ba ne mu sake dawowa a zaɓen 2027 wanda ko da rai ma a lokacin ba mamaki mu na wani aikin na daban ko ba wannan aikin a ka tura mu ba. Idan akwai wani wa’azi da ya dace kullum mu riƙe shi a matsayin tunatarwa shi ne mutuwa wacce marigayi Alhaji Adamu Danmaraya Jos ke cewa “mutuwa rigar kowa… da da hali da sai in tuve amma babu hali” haka kuwa a ka yi Ɗan Maraya ya koma ga mahalicci don rigar mutuwa ba zai yiwu a kwave ta ba. Yau a ka fara yin mutuwa?

A’a don tun tarihin ’ya’yan baban mu Annabi Adamu AS wato Ƙabila da Habila a ka fara samun wannan mutuwar kuma kullum ɗauka ta ke yi ba ta gajiya ba ta ritaya kuma ba ta tsufa! Me zai sa mutum in haka ne ya warware kafa a duniya ya manta cewa ba madauwama ba ce. Haƙiƙa in wani zai dauwama a duniya bai wuce fiyeyyen halitta Annabi Mai Tsira da Aaminci ba.

Duk tarihin da mu ke samu na manyan bayin Allah da su ka koma ga Allah a nan doron duniya su ka rayu kuma su ka yi ’yan shekarunsu zuwa wa’adi su ka koma. Mu ma haka ne ba za mu kaucewa wannan wa’adi ba. Kowace rai ta na da ajali da kuma sanadiyyar hanyar tafiya.

Kazalika in lokaci ya yi sai tafiya ko mutum lafiyar sa kalau kamar taken labarin nan na Magana Jari Cen a marigayi Malam Abubakar Imam “in ajali ya yi kira ko ba ciwo a je” yaya mu ka iya ban da mu zama masu kanakan da kai da kyautata fatar samun rahama daga wajen mai duka.

Ni dai na kan shiga matuƙar juyayi musmamman in na tafi maƙabarta don ziyara ko yin sutura ga wani da Allah ya karva. Wani lokaci na kan tsaya har mutane su ragu a bakin kaburbura ina cikin tunani na mu ma nan ɗin za mu dawo don kuwa ai waɗanda su ke cikin ramukan nan da a saman ramukan su key au kuma ga sabon gidan su na gaskiya.

Kar na yi ta shunfuda ban gabatar da bayani kan marigayi Shehu Saulawa ba wanda kwarerren ɗan jarida ne da ya yi fice musamman lokacin da ya yi aiki da sashen Hausa na BBC. Sunan sa ya kara fitowa lokacin da a ka fi samun rikici a Jos jihar Filato inda a kan samu asarar rayuka kan bambancin addini da kuma ƙabilanci.

Saulawa ya zama mai dauko labaru daga Filato kafin tsanantar rikicin ya sa shi hijira zuwa Buachi inda ya cigaba da rayuwa har ya zama tamkar mahaifarsa jihar Katsina. Gaskiya ma an fi sanin Shehu Saulawa a Bauchi fiye da jiharsa ta asali wato Katsina.

Tun ina ƙarami a Gombe na san Shehu Saulawa don in a na muhimman taruka da matsayin su ya kai a ɗauki labaru irin na ƙasashen ƙetare ya kan zo Gombe ya ɗauki labarun. Lokacin tsakani na da shi na kalle shi a matsayin ƙwarerren dan jaridar duniya kuma mu gaisa kafin mu sake gamuwa.

Maganar ko wataran za mu yi hulɗa ko ma zai buga min waya bai ma taso ba ashe kuwa za a wayi gari har Saulawa ya ji ya na kaunata da kuma ba ni kwarin gwiwar yin wannan aiki na jarida ko aika rahotanni kan muhimman lamura daga Nijeriya. Duk lokacin da na gamu da Saulawa za ka ga ya na murmushi kuma har mu tuna wani rahoto mai ɗaukar hankali da a ka yayata mu ɗan yi sharhi a kai.

Wataran Saulawa ya zo Abuja wani aiki sai na kai ma sa ziyara masaukinsa inda ya bayyana min zai huta da aikin BBC zuwa wani aikin na daban. Na yi ma sa fatan alheri duk da ko a lokacin ina ga bai gaji ba don alamar gajiya a lokacin ba ta nuna a fuskar sa ba. Ba a daɗe ba marigayi Shehu Saulawa ya koma ma’aikacin rediyon Faransa na wasu shirye-shirye na musamman ba lalle aika rahotanni nay au da kullum da ke buqatar matuƙar kuzari da nazari dare da rana ba.

A duk lokacin da aikin jarida ya ratsa jinin mutum to zai yi wuya a dau lokaci ba tare da ya yi mafarkin ya tafi wani taro ya na ɗauko rahoto ba. Kazalika mawuyacin lamari ne ga duk ɗan jarida mai nazari dare da rana ya share shekaru 10 ya na aikin ba tare da ya fara farin gashi ba.

Na zauna da ’yan jarida da dama na ga hakan. Tunanin irin waɗannan ’yan jarida ta yaya za su samu labarin da ya gagari kundila kuma su bayyana shi cikin sahihanci ya kuam yi tasirin da a ke buƙata na kawo sauyi mai ma’ana. Wato in wata zamba a ke yi ko zalunci to a sanadiyyar labarin a samu sauƙi ko ma a magance matsalar kakaf.

Saulawa ya yi fice wajen haɗa rahoto da amfani da ’yan kalmomi kaɗan amma hakan ya isar da duk saƙon da a ke buƙata. Duk mai sauraron rahotannin marigayin zai amince da ni cewa ya gwanance wajen taƙaita bayani da muryoyin da ya kan goya a rahotanninsa.

Abun buƙatar mai sauraron rediyo ya samu gamsashshen bayani da amfani da dukkan muryoyin da a ke buƙata kuma a ’yan mintuna biyu zuwa da rabi ko ma na juyo baya a minti ɗaya zuwa daya da rabi. Fasalin irin rahotannin manyan kafafen labaru da kwararrun ’yan jarida irin Saulawa su ka tabbatar da hakan.

A baya zai yi wuya na amince za a wuni a na wani taro amma a cikin minti biyu wakilin kafar labaru ya ba da labarin har ya zama ko wanda ya je taron ya gamsu da cewa iya muhimman abubuwan da a ka aiwatar kenan. Hakanan shi rahoton rediyo na da bambanci da na talabijin don yayin da a talabijin a na iya kallon hoto kuma hoton kaɗai ya isa ya ba da labari ko ba a ce komai ba, a rediyo sautin ne zallah da sai wakilin da ya kware zai yi amfani da tsarerren rubutu da sautuka wajen ba da bayani da hoton abun da ya faru a sautance har mai sauraro ya ji kamar ya na kallon abun da ke faruwa ne.

Zumuncin Shehu Saulawa ya kai don ko ni na shaide shi da ziyara kama daga ta kafa takanas ta Kano har ma ya ɗauki wayarsa ya buga kuma zai yi wuya ka buga wayar marigayin hatta lokacin ba shi da lafiya bai ɗauka ba.

Na yi farin ciki duk da ina cikin juyayi yanda wakilin Muryar Amurka a Bauchi Abdulwahab Muhammad ya zo tare da marigayi Shehu Saulawa su ka yi min ta’aziyyar rasuwar mahaifi na Alhaji Adamu Muhammad Maigoro a 2020.

Saulawa har ɗakin mahaifiyata ya shiga ya yi ma na ta’aziyya da addu’a. Yau ga mu nan mu na juyayi da yin addu’ar Allah ya jikan Shehun ‘yan jarida.

Kammalawa;

Daga bara zuwa bana an samu rashin fitattun ’yan jarida na yankin arewacin Nijeriya. Wasu jinya su ka yi wasu kuma hatsarin mota ne ya yi sanadiyyarsu. Ba za mu manta da Danladi Ndayako da abokin tafiyarsa Muhammad Isa ba waɗanda su ka rasu bayan hatsarin mota a hanyar Minna. Ga ma wakilin AIT a Minna Muhammad Danladi Ibrahim.

Ga irin su Musa Tijjani da Bashir Baba da su ka yi jinya. Ɗan jarida ko duk mai wata sana’ar daban da ma duk mai rai mu sani aro ne Allah ya ba mu kuma zai karɓe kayansa wata rana. Don haka mu yi ƙoƙarin shuka alheri don ana yi wa alheri kirari da ‘Gadon barci’.