Shin ragwanci ke haddasa ta’addanci?

Daga NASIR ADAMU EL-HIKAYA

Da mamaki ainun a iya zayyana ‘yan ta’adda da ragwage don ko banza suna himma wajen aikata miyagun ayyuka. Wasunsu ma ba sa barci ido biyu rufe ko kuma su kan sha ƙwaya a yawanci lokuta don kar barci ko kasala ta ɗauke su wasu abokan hamayya ko ma jami’an tsaron gwamnati su cim masu.

Kazalika, wasu mutanen kan iya zama ragwage a wasu lamuran da ba sa ƙauna ko son zuciyar su ya saɓa da abun da a ke so su yi na addini ko al’ada. Misali a nan kamar tafiya masallaci don sallah, gaida maras lafiya, ziyarar sada zumunci, raka mamaci makwanci da sauran su.

Wasu mutane kan nuna kasala ga irin waɗannan muhimman lamura a rayuwa amma in ka duba abubuwan da ran su ke so za ka ga himmar su. Misali, zama minti 90 don kallon ƙwallo, fim mai minti 180, shagali a kulob, bukin murnar ranar haihuwa da soyayyar maza da mata da makamantan su. 

Wani babin ma shi ne yadda masu hannu da shuni ke nuna kasala in za su yi wani aiki da ya shafi talaka kuma ba za a samu ribar sa a kasuwanci ko siyasar su ba sai gobe ƙiyama. Za ka ga waɗannan bayin Allah ba sa kuzarin shiga irin wannan abubuwa masu dogon zango wajen ganin lada ko la’ada.

Alƙiblar wannan mako na son tsokaci kan kalaman shugaba Buhari a murnar babbar sallar bana inda ya yi magana kan ragwanci da ya ke ganin shi ke hana mutane da dama samun dukiya ko abinci ta hanya mai kyau.

Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya ce wasu mutane ragwanci ke hana su neman abinci ta hanyar halal har hakan ya kai su ga shiga miyagun ayyuka.

Shugaban na magana ne bayan samun rahoton da ke nuna kashi 2.5% na faɗin ƙasar nan ne a ke amfana da shi wajen aikin noma.

Da ya ke amsa tambaya daga manema labarai a murnar babbar sallah a Daura, shugaban ya buƙaci ‘yan Nijeriya su ƙara dagewa wajen amfana da albarkar faɗin ƙasa wajen neman abun dogaro da kai.

Shugaban wanda tun a shekarun baya ya zayyana wasu matasan Nijeriya da cewa su na da kasala, ya ƙarfafa matsayar ta sa ga nuna ragwanci na daga dalilan shiga miyagun ayyuka.

Kasancewar shugaban ya yi maganar a taƙaice, mai taimaka ma sa ta fuskar yaɗa labarai Garba Shehu ya yi ƙarin bayani inda ya fito da batun rahoton da a ka kawo wa shugaban na ƙarancin amfani da filayen noma. Wannan ya nuna mutum ka iya ratsawa dazuka ba zai ga komai ba sai bishiyoyi dashen Allah da ramukan da kuregu suka tona!. Wasu kuma dazukan sun zama mafaka ga gaggan ɓarayi da ‘yan ta’adda.

Duk da akwai jihohin da ke da zaman lafiya da yanzu haka a ke noma, akwai da dama waɗanda shiga daji kan zama tarko mai haɗari. Mutane da dama sun shiga dazuka don noma amma wa imma miyagun iri su sace su ko kuma a tsinci gawar su.

Haka nan, lamunin noma da a ke bayarwa bai faye shiga noman ba sai wasu lamura na daban da suka haɗa da gina gidaje da sayen babur ko mota.

Ina ganin wata hanya da za ta zama mafita ita ce ta amfani da matasa a dukkan ƙananan hukumomi wajen buɗe gonakin gwamnati don gudanar da noma. A watannin baya gwamnatin Nijeriya ta hannun ma’aikatar ƙwadago ta ɓullo da wani shiri na ɗaukar matasa dubu ɗaya a kowace ƙaramar hukuma da ba su aikin wucin gadi inda za a riƙa biyan su wajajen Naira dubu 20 a wata.

Na bincika wasu daga matasan shara suka riƙa yi a matsayin aikin wucin gadi. Me zai hana Gwamnatin Tarayya ta ma’aikatar noma ta ɓullo da shirin ɗaukar matasa aikin wucin gadi ta riƙa biyan su mafi ƙarancin albashi a wata da a zahiri bai fi dubu 20 ɗin ba su noma gonakin da gwamnati za ta samar.

Kowane matashi a tabbatar ya noma aƙalla buhu 5 na amfanin gonar da ya ke da yabanya a jihar su kamar masara, gero, dawa, wake, rogo, shinkafa da sauran su. Gwamnati za ta raba iri mai inganci da kuma dabarun noman zamani. Da zarar an yi girbi, gwamnati ta kwashe kashi 50% na amfani ta adana a rumbunan ta, ta bar wa matasan kashi 50%. Idan an jera shekaru biyar a na haka matasa za su koma haziƙan manoma kuma sabon rahoto zai nuna a na amfana da albarkar ƙasar noma a Nijeriya yadda ya dace.

Da rani za a koya wa matasan noman rani ko kiwon kifi bisa raba riga tsakanin gwamnati da matasan. In wannan ya ɗore za a wayi gari akasarin matasa na da sana’a kuma ba za su samu lokacin banza da miyagun iri za su cusa su cikin gungun su ba. 

Duk wanda ya ji daɗin wannan sana’a zai jawo abokan sa don su ci ribar tare. Hatta ɓarayi da suka maida daji mafaka za su iya zaɓar maida mafakar gona. A ƙarshe sai ka ga bawan damuna ya zama baturen rani ko kuma bawan rani da damuna ya zama baturen rani da damuna.

Gwamnati a yanzu ba ta sha’awar ɗaukar ma’aikata don haka sai ta ƙirƙiro hanyoyin samun ayyukan dogaro da kai da za su rima samar da riba ninkin ba ninkin albashi. Wasu mutanen Nijeriya sun zama tamkar kazar da ta kwana kan dami ne ba ta sani ba. Wasu kuma sun san a kan dami su ke kwana amma don ragwanci ba za su iya taɓukawa su kunce igiyar damin don samun amfanin da za a sussuka don samun tuwo mai laushi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *