Daga HASSAN IMRAN
Assalamu Alaikum, ‘yan’uwana. Yau na zo da wata taƙaitacciyar nasiha ne akan illolin masu da’awar cewa mace na da hurumi da kuma daidaituwa da maza, da nufin ba da shawarwari da samar da mafita.
Daga cikin ƙalubalen dake addabar al’ummar yankin Arewa akwai matsalolin zamantakewar aure. A shekarun baya, mata sun kasance masu biyayya kuma masu kula da tarbiyyar ‘ya’yansu wanda hakan ya taimaka wajen gina Ingantacciyar al’ umma da ‘ya’ya masu albarka. Hakan harwayau ya taimaka wajen inganta cigaban da ‘yan Arewa suka riƙa samu a matakai daban-daban, duk da kallon komabayan da ake yi mana. Daga baya, sanadiyyar cigaban fasahar sadarwa da aka samu, akasarin jama’a musamman matasa sun karkata ga amfani da zaurukan sada zumunta, hakan kuwa ya haifar da matsaloli a yanayin tarbiyyar ‘ya’yan Musulmi, musamman ‘yan Arewa.
Abin takaici da ban haushi, waɗanda ya kamata a ce suna inganta tarbiyya su ne suka zama masu fakewa da guzuma suna harbar karsana. Akwai wani shiri da tashar talabijin ta Arewa 24 ke yaɗawa wanda suke wa laƙabi da ‘Shirin Mata A Yau’. A wannan shirin, akan gayyaci masana daga ɓangarori daban-daban domin tattaunawa kan wasu batutuwa da suka shafi mata, da zamantakewarsu a gidajen aurensu. Sai dai a maimakon wannan shiri ya inganta tarbiyyar mata, sai kuma ya juya yana rushewa, ta hanyar cusa wasu mummunan ra’ayoyi masu masu goyon bayan aƙidar feminism – waɗanda ke da’awar kare haƙƙin mata. Wannan shiri yana ƙoƙarin hurewa mata kunne wajen bijirewa mazajensu da kuma koya musu halayyar rashin ɗa’a.
A kwanakin baya akwai wata muhawara da ta ja hankalin mutane a shafukan sada zumunta wacce ta samo asali daga cikin wannan shiri, inda aka riƙa tattaunawa kan shin mace ce ya kamata ta fara gaishe da mijinta ko kuwa namiji ne? A ra’ayin masu gabatar da shirin Mata A Yau, idan mace bata gaishe da mijinta ba, me zai hana shi mijin ya gaishe da matarsa?
Eh, mun sani gaisuwa abu ne mai kyau da musulunci ya karantar da mu kuma ya kwaɗaitar da mu akai. Hakazalika ya nuna mana cewa yaɗa gaisuwa na ƙarfafa kyakkyawar zamantakewa da zaman lafiya. Manzon Allah (SAWA) yayin da yake bayani game da girman haƙƙin miji yake cewa, “Da ina da ikon in sa wani ya yi wa wani sujada, da na umarci mace ta yi wa mijinta sujada.”
Wannan hadisin yana karantar da mace muhimmancin girmamawa da kuma darajanta mijinta. Ya kamata mata su sani cewa, biyayya da kuma bin mazajensu yadda suke so, shi zai ƙara musu danƙon ƙauna da kuma kyakkyawar zamantakewa a tsakanin su a matsayinsu na ma’aurata.
Wannan ita ce hanya mafi alkhairi da mace za ta mallaki mijinta ta zama abokiyar tafiyarsa, ba abokiyar hamayya ba. Kuma namiji na iya kashe dukiyarsa akan matarsa muddin tana masa biyayya kuma zai bata kulawar da yakamata.
A makon da ya gabata ne, tsohuwar jarumar Kannywood, Mansurah Isah, ta bayyana cikin wani bidiyo da ta wallafa yadda mata ke shiga mawuyacin hali bayan mutuwar aurensu. Ta shawarci mata da su kasance masu haƙuri a gidajensu na aure tare da gujewa duk wani abu da ka iya kawo musu ɓaraka a ɗakunan mazajensu. Ta yi gargaɗin cewa babu komai a rayuwar zawarci sai tarin baƙinciki da da-na-sani.
A fahimta ta hanyoyin magance matsalar zamantakewar aure shi ne, ma’aurata maza da mata su san haƙƙokin da Allah ya rataya a kafaɗunsu. Ma’aurata su sani cewa aure ibada ne kuma hanya ce da mutum zai iya samun aljanna in sun kula waɗannan haƙƙoki.
Lallai akwai buƙatar hukumomi da masu faɗa a ji su ja hankalin shugabannin tashar Arewa 24 akan illolin yaɗa irin waɗannan munanan aƙidu na Feminism da makiya ke so su yaɗu a cikin al’ummar musulmi. Haka kuma, akwai buƙatar gwamnati ta ƙara ƙarfafa Hukumar Hisba ta hanyar kula da kuma sa’ido akan masu ruguza tarbiyyar ‘ya’yan al’umma. Makarantu da malamai yakamata su mayar da hankali wajen karantarwarsu da hudubobinsu domin gyara tarbiyyar al’umma.
Allah Ya kawo mana ƙarshen wannan matsalar zamantakewar aure kuma ya zaunar da ƙasarmu lafiya. Amin.
Hassan Imran ya aiko da wannan nasiha ne daga Jos, kuma za a iya samun sa kan adireshinsa na imel kamar haka: [email protected]