Cire tallafin fetur alkairi ne ga gwamnoni – Uzodimma

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodimma, ya ce cire tallafin man fetur alheri ne ga gwamnatocin jihohi.

Gwamnan, wanda ya yi magana a ranar Litinin ɗin da ta gabata a jihar Imo yayin da yake duba wasu ayyuka na murnar cika shekara ta farko a wa’adinsa na biyu, ya ce, yanzu haka akwai ƙarin kuɗaɗe da ke cikin asusun gwamnatocin jihohi domin ci gaban jihohinsu.

“Abin alheri ne kai tsaye, ba abin kunya ba ne ga ’yan ƙasa domin yanzu an samu karin kudade a jihohi kuma dole ne gwamnatocin jihohi su yi wani abu don nuna wa ‘yan kasa cewa za su iya yin wadannan abubuwa domin a yanzu suna samun karin kuɗaɗe a matsayinsu na gwamnati. sakamakon cire tallafin man fetur da Gwamnatin Tarayya ta yi.”

Uzodimma dai ba shi ne gwamna na farko da ya yi irin wannan ikirarin ba.

A shekarar da ta gabata ne Gwamna Abdullahi Sule na Jihar Nasarawa ya bukaci ‘yan Nijeriya da su yi wa Gwamnoni hisabi kan yadda aka inganta kuɗaɗen da aka samu daga asusun tarayya.

Sule ya bayyana haka ne a lokacin da yake amsa tambayoyi a wata hira da gidan talabijin na Channels TV’s Politics Today.

Ya ce jama’a na shan wahala, inda ya buƙace su da su tambayi gwamnonin jihohinsu ko me suke yi da ƙarin kuɗaɗen shiga daga gwamnatin tarayya.