Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Bankin Dunya ya ce kuɗaɗen kasafin da gwamnatin Nijeriya ke kashewa kan shirin walwalar jama’a bai kai yawan na sauran ƙasashen hamadfar Afirka ba kuma bai yi wani tasiri wajen talauci ba a ƙasar.
Cikin wani sabon rahoto, bankin ya ce kasafi na 0.14 cikin 100 na arzikin cikin gida na Nijeriya bai kai 1.1 ba da sauran ƙasashen Afirka suka saba warewa duk shekara domin inganta rayuwar ‘yan ƙasarsu.
Rahoton wanda ya duba dukkan shirye-shiryen da gwamnatin Nijeriya ke aiwatarwa, ya nuna cewa talauci ya ragu ne da maki 0.4 kacal a Nijeriya.
Kasafin ya yi ƙasa sosai, inda wasu bayanai daga cibiyar ƙwadago ta duniya ILO suka nuna bai wuce kashi 0.45 ba duk shekara tun daga 2010 zuwa 2021.
Duk da cewa akwai alƙaluma daban-daban, bayanai a 2019 sun nuna kasafin a kan kashi 0.7 cikin 100 na arzikin cikin gida idan aka cire ɓangaren lafiya.
