Shugabancin MOPPAN: Ahmad Sarari ya kafa sabon tarihi a Kannywood

Daga AMINA YUSUF ALI

Shugaban Haɗaɗɗiyar Kungiyar Masu Sana’ar Shirin Finafinan Hausa ta Nijeriya (MOPPAN) mai barin gado, Dr. Ahmad Muhammad Sarari, ya kafa wani sabon tarihi a masana’antar shirin fim ta Kannywood, inda ya zama shugaban ƙungiyar na farko da ya fara sauka daga muƙaminsa ba tare da ya ƙara ko da kwana ɗaya ba.

A tarihin ƙungiyar, wacce aka kafa ta tun a farko-farkon shekarun 2000 kuma ta samu aƙalla shugabanni guda biyar a shekaru 17, ciki har da Sarari, daga wanzuwarta zuwa yanzu, babu wanda ya samu ikon sauka daga muƙamin shugabancin a lokacin da wa’adinsa ya cika, kamar yadda kundin tsarin mulkin ƙungiyar ya tanada.

Yayin da wasu dag cikinsu sai an yi kama-kama da taron dangi tsakanin ƙungiyar da iyayenta ake iya sauke su, wasu kuwa dai su kan wuce wa’adin ƙa’idar ne kafin su sauka daga mulkin.
A jawabin bankwana da Sarari ya aike wa mambobin ƙungiyar ranar da wa’adin nasa ya cika, wato a Talatar da ta gabata, wacce ta zo daidai da 19 ga Oktoba, 2021, ya yi bayani kamar haka;

“Assalamu alaikum, abokan aiki da abokaina. Alhamdulillah! Yau ce ranarmu ta ƙarshe a matsayinmu na shugabannin Ƙungiyar MOPPAN ta ƙasa. Kamar yadda na kusa da ni suka riga suka sani, ni ban iya yin bankwana ba. Don haka nake bayar da haƙuri ga waɗanda wannan jawabi nawa ya ɓata wa rai. Kuma ina da mutane da dama da nake son na gode wa saboda goyon baya da kuma jajircewarsu. Wanda ba don su ba, da ba za mu cimma nasarorin da muka cimma a wannan ƙanƙanin lokacin ba. 

“A gaskiya ina alfahari da aiki tare da waɗannan dandazon mutane masu ƙarko da hangen nesa kuma in alfahari da nasarorin da muka samu tare da su a ƙungiyance. A yanzu haka ku kun ƙara samun fahimta a game da yadda za a jagoranci katafariyar ƙungiya kamar MOPPAN.

“Haƙiƙanin gaskiya na ji daɗin kasancewa tare da ku. Kuma sannan aikin da muka yi da kuma nasarorin da muka samu tare da ku. A yanzu zan bar wannan kujera tawa tare da yaƙinin cewa, ‘yan baya za su yi ƙoƙari wajen shallake dukkan siratsi da kuma kawar da dukkan matsalolin da ka iya zuwa. Mun yi ƙoƙarin wajen ganin mun zaɓo jajirtattun mutane waɗanda suka dace don ba da gudunmowar hikimomi masu inganci don ciyar da MOPPAN gaba. Wannan ya sa ni alfahari da godiya marasa iyaka. 

“Ga waɗanda suka tsaya takarar neman muƙamai a kakar zaɓen MOPPAN mai zuwa, ina yi musu fatan alkhairi. 

“Kamar yadda masu magana suke cewa, wai shi zumunci a zuci yake. Mu ci gaba da riƙe zumunci. Kuma zumunci umarni ne daga Allah S.W.T.

“Daga ƙarshe, ina neman afuwa daga waɗanda na ɓatawa, da sani na, ko ba sani na. Ni kuma a nawa ɓangaren, na yafe wa kowa.”

Bayanai sun tabbatar wa da Manhaja cewa, an bai wa Kwamitin Zaɓe na MOPPAN wa’adin kwanaki 30 ya gudanar da sabon zaɓen shugabannin da za su riƙe ragamar mulkin a zango na gaba. Shi dai Ahmad Sarari yana da damar sake tsaya wa takara a karo na biyu, saboda a yanzu zango guda kawai ya yi, kamar yadda kundin mulkin ƙungiyar ya tanada.