Sin na adawa da yadda NATO ke ta ƙiyayya tsakanin manyan rukunoni a faɗin duniya

Spread the love

Daga CMG HAUSA

Kwamitin sulhu na MDD ya kira taro kan batun Ukraine a jiya Alhamis, inda zaunannen wakilin ƙasar Sin dake majalisar Zhang Jun, ya yi kira ga ƙasa da ƙasa da su rubanya ƙoƙarinsu wajen sa kaimi ga tsagaita buɗe wuta a tsakanin ɓangarorin da abin ya shafa. Ya kuma bayyana cewa, akwai darasi a cikin matsalar Ukraine, don haka ya kamata a yi tunani a kansa sosai.

Ban da wannan kuma Zhang ya nuna cewa, ƙungiyar NATO na habaka zuwa gabas bayan yaƙin cacar baki. Ya ce NATO ƙungiyar tsaro ce, amma tana ta tada yaƙe-yaƙe a wasu kasashe masu ikon mulkin kai, lamarin da ya haddasa mutuwa da jikkatar dimbin mutane da ma haɗarin jin kai.

Zhang ya jaddada cewa, tun tuni aka kawo ƙarshen yakin cacar baki, kamata ya yi ƙungiyar NATO ta daidaita manufofinta don dacewa da halin da ake ciki yanzu.

Zhang ya kuma bayyana cewa, ƙasar Sin ta yi kira ga ƙasa da ƙasa da su cika alƙawarin da suka yi wa babbar manufa da ƙa’idojin kundin tsarin MDD, da mutunta ƙa’idar kiyaye tsaron kai ba tare da lahanta tsaron sauran ƙasashe ba, da hada kai ta hanyar yin shawarwari, a ƙoƙarin kafa tsarin tsaro mai daidaito da ɗorewa na shiyya-shiyya da duk duniya, ta yadda za a iya warware matsalolin tsaro da bil Adama ke fuskanta, tare da neman samun zaman lafiyar duniya mai ɗorewa.

Mai fassarawa: Kande Gao

By Editor