Sin tana sa lura ga yanayin da ake Ciki a Burkina Faso

Daga CMG HAUSA

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen ƙasar Sin Mao Ning, ta ce Sin tana sa lura game da yanayin da ake ciki a ƙasar Burkina Faso bayan da aka yi juyin mulkin soji a ƙasar, kana tana son yin ƙoƙari tare da sassan ƙasa da ƙasa, wajen taimakawa ƙasar kaiwa ga cimma samun zaman lafiya da bunkasuwa.

Mao ta bayyana hakan ne a gun taron manema labaru da aka gudanar a yau Asabar.

Jami’ar ta kara da cewa, Sin ta lura da yadda Burkina Faso, ta sanar da ci gaban ta, da bin jadawalin wucin gadi da ƙungiyar ECOWAS ta cimma daidaito kan sa a baya, tana kuma girmama zaɓen jama’ar ƙasar Burkina Faso, da yin imani da cewa, jama’ar ƙasar za su iya daidaita harkokin cikin gidan su da kansu, da kuma cimma nasarar wanzar da zaman lafiya da lumana.

Mai fassara: Zainab