Ku guji amfani da ‘yan daba don tada tarzoma yayin zaɓe – CP Abubakar Lawal

Daga BABANGIDA S. GORA a Kano

Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Kano CP Abubakar Lawan ya gana da shugabannin jam’iyyun siyasa da suke zaune a Jihar Kano a kan shirye-shiryen da ake yi na fara yaƙin neman zaven 2023.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar da yammacin ranar Talata.

Ya ce kwamishinan ‘yan sandan Jihar Kano CP Abubakar Lawan “ya yi godiya a gare su bisa amsa kiran da suka yi domin tattaunawa a kan gayyatar.

Haka zalika ya umarci shugabannin jam’iyyun da su kawo jadawalin yadda za su gudanar yaƙin neman zaɓen na su, don tabbatar da bawa kowa tsaron da ya kamata.

“Sanarwar ta ja hankalinsu da su kwaɓi magoya bayansu da kada a samu matsala wani ya yi abinda bai kamata ba, tare jan hankalin sojojin baka da suke amfani da kalamai na cin zarafi da cin mutunci da su daina.

Rundunar ‘yan sandan Jihar Kano ta gargaɗi matasan da suke ɗaukar makamai da kuma ta’ammali da kayan maye cewa rundunar ba za ta kyale duk wanda aka samu ba domin za a kama shi tare da gurfanar da shi a gaban kotu.

Rundunar ta ja hankalin masu ababen hawa da su tabbatar da cewa akwai lamba a jikin ababen hawan nasu.

A ɓangaren shugabancin jam’iyyun sun tabbatar wa da rundunar cewa kansu a haɗe yake kuma za su tabbatar an yi komai cikin kwanciyar hankali da lumana don ci gaba da samun zaman lafiya a faɗin Jihar Kano.

A ƙarshe rundunar ta bayar da lambobin waya ga dukkan wanda yake da ƙorafi ko zargi ya yi gaggawar sanar da ita domin ɗaukar matakin da ya dace.