FIRS ta gargaɗi hukumomi da ma’aikatun gwamnati kan katsalandan a harkar haraji

Daga AMINA YUSUF ALI

Hukumar tattara haraji ta Nijeriya (FIRS) ta gargaɗi hukumomin gwamnati a kan tsoma baki a harkar haraji. Wato ɗora haraji, karɓar harajin da bibiyar waɗanda ba sa biyan harajin.

Wannan jawabi dai ya fito daga shugaban zartarwa na hukumar FIRS, Mista Muhammad Nami. Kamar yadda yadda kamfanin dillancin labarai ya rawaito.

Mista Nami ya ya yi ƙarin jan kunne ga hukumomi da ma’aikatun a kan yadda suke ɗaukar ma’aikatan da za su dinga karɓar harajin da gwamnatin tarayya take bin kamfanoni da mutane, masana’antu bankuna, da sauran cibiyoyin gudanar da kasuwanci ba bisa tsarin doka ba.

Nami ya bayyana damuwarsa a ka yadda wasu mahukunta a wasu ma’aikatun gwamnati suke yi wa hukumar FIRS katsalandan wajen karɓar harajin da sauran abubuwan da suka shafi harkar harajin. Har ta kai ta kawo a cewar sa, wasu hukumomin sukan ƙulla yarjejeniyar haraji tare da mutane.

A cewar Mista Nami, hakan ya saɓa wa dokar Nijeriya ta sashe na 68(2) na kundin tsarin mulkin Nijeriya da ya bayyana FIRS a matsayin babbar hukumar dake da alhakin amsar haraji da sauran harkokin da suke da alaƙa da shi.

Sai dai kuma sashen dokar ya bayyana cewa, sai dai idan wani umarnin ne ya zo daga Ministan kuɗin tare da Sahalewar majalisar dokoki akasin haka zai iya faruwa.

Hakazalika a cewar sa, sashe na 12(4) dokar ta ƙara haramta ƙarara kada wata hukuma ta amshi haraji idan ba FIRS ɗin ba.

A ƙarshe ya bayyana cewa, a yanzu haka, hukumar ta shirya tsaf don fara tilasta biyan harajin daga mutanen da aka yi wa ragi ba bisa doka ba, da waɗanda ma basa biya a faɗin jihohin Nijeriya da ƙananan hukumominta.