Siyasar Nijeriya: Har yanzu kamar an gudu ba a tsira ba

Bisa ga dukkan alamu dai sake maimaita aji za a sayi. Ma’ana a yunqurin talakawa na hutawa da mulkin ɗan Jummai kuma a sake ɗauko ɗan Juma.

Al’umman Nijeriya na buƙatar canji, amman har yanzu ba su ɗauko canji ba. Har yanzu al’umma na cikin ruɗu. Kuɗi da ƙabilanci sun yi musu kanwaya, gaba ɗaya kowa ya ruɗe. Wasu suna bin mayaudara, wasu na bin mawaƙa, wasu kam har yanzu suna bin jahilan malamai.

Yaushe malamin da ya ke ɗan siyasa zai gaya maka gaskia akan wanda zaka zaɓa? Yaushe mawakin da kuɗi ya ke nema zai gaya maka gaskia akan wanda zaka zaɓa? Yaushe mayaudari da shi kawai mulki ne buƙatar sa zai maka abin kirki?

A yanzu, Ibo sun ce wannan shine nasu mai gaskiya. Ana su tunanin Pita Obi zai sake musu hanyar zuwa kasan waje, domin kullum suna ganin zuwa ƙasar waje shine wayewa. Wasu na ganin Ɗan musa, domin yana kai mutane karatu a kasar waje, suna ganin hakan shine ci gaba. Wasu na ganin APC, wasu kuma a ruɗe suke. Kowa da abinda ya ke ran sa. Inma ƙabilanci, ko batun Adddini, wasu suna ganin cancanta, to har yanzu ba a san wanda ya cancanta ba.

Mu koma baya, mai karatu bani hankalin ka, domin tuna shekaru 10 baya. Me ya faru a lokacin? Muna ta ganin Buhari shi ne mai gaskiya, Ebele mara gaskiya ne, sai aka zo aka gani Buharin ya nunka Jonathan ba rashin gaskiya. Amman mecece gaskiyar da ake buƙata? A kullum kowa gaskiyar ƙabilanci ya ke bi.

Saboda Buhari ɗan Hausa ne, kuma musulmi shi ne ya sa yafi Jonathan gaskiya, masha Allah, ga irin gaskiyar ai, kowa yana samun adalci. Babu makaranta, abinci ya yi tsada, babu wutan lantarki, man fetur yayi tsada, komai na rayuwa ya ƙara tsada, to me ya faru? Ina gaskiyar ta baba? Shin an daina samun hare-haren? Daman kafin zuwan Buhari ana kashe kashe a Katsina da Zamfara da Sokoto? Masu tunani za su ce ba Buhari bane sanadi, eh kuma haka ne, ba daga shi ba ne to ina ne matsalar ta ke?

Mai tunani sa hankalinka da kyau ka gani. Ana kashe-kashe a Nijeriya, don Allah da me ake kashe-kashe? Su wanene ’yan bindiga kuma a ina suke zama a Nijeriya? Su waye iyayen su, mene ne buƙatarsu. Wannan wurare da suke kai hare haren me suke nema a wajen. Me ya ke haifar da hare-haren, wa ya goya musu baya? Me ya sa har yanzu sun gagari sojojin Nijeriya? Shin sojojin mu ne ba su da ƙoƙari, koko a rogaye ne? Shin ka tava kawo wannan a kanka?

Saboda gwamnatin ma an ɗaura ta ne akan wata turba. Wannan turba ɗin wa ya ɗora ta a kai? Babu wanda ya sani. Kuma a hakan wai muna tunanin samun sauƙin nan gaba.

Mai karatu, wallahi, tallahi, idan ba Allah ne yaji tausayin mu ba, shugaba da zai zo nan gaba, mukinsa sai yafi na konne raɗaɗi. Ko muna so, ko bamu so, muna vata lokacin mu ne, domin wallahi tallahi bisa ga dukkan alamun abubuwa da suke faruwa zamu sake maimaita aji ne. Idan baka gane ba mu haɗu a mako mai zuwa dan kaji ainihin in da matsalar ta ke.

Daga Mohammed Albarno. O8034400338, [email protected].