Gidauniyar Zakka da Waƙafi ta bai wa ƙungiyar mata tallafin itatuwan waƙafi

Daga AMINU AMANAWA a Sakkwato

A ƙoƙarin Hukumar Zakka da Waƙafi ta Jihar Sakkwato na haɓaka tattalin arzikin al’umma musamman marasa galihu da marayu da zawarawa da inganta yanayin ƙasa, ya sa aka bada iraruwan itace ga wata ƙungiyar mata mai taimakon marayu, zawara da mabuƙata, ƙungiyar ta rayuwar mata wadda ke da makarantar Raoudatoul Ibadurrahmane da ke a garin Maradi jamhuriyar Nijar.

A shekara ta 2016 sun ziyarci Jihar Sokoto inda suka ziyarci mai martaba sarkin Musulmi, ma’aikatar lamurran addini da ta mata tare da gidauniyar Zakka da Wakafi ta jihar Sakkwato, inda suka buƙaci haɗa kai da ƙarin hulɗa musamman wajen taimakawa marayu, zawarawa, marasa hali da kuma ayukkan Da’awa, yayin da shekara ta 2017, suka gayyaci Shugaban Zartarwar Hukumar a Maradi inda ya gabatar da kasida mai taken, ‘Gudun mawar iyaye cikin matsalolin Tattalin Arziki ‘ yayin da a cikin watan mayu na wannan shekara 26/05/2022 sun rubuto buƙatar da Hukumar Zakka da Wakafi ta tallafa masu da iraruwan itatuwa na Dabino da Sauran su, don su shukka a makarantun su, da sauran su, kana da rabawa a wasu muhimman mutane da kuma mambobin ƙungiyar.

Shugaban Zartarwar Hukumar Zakka da Wakafi ta jihar Sokoto malam Muhammad Lawal Maidoki Sadaukin Sakkwato ya aminta da sashen Wakafi da ya tallafa masu da iraruwan.

A ranar Lahadin 14/08/2022 wakilin shugaban ya gabatar da iraruwan itatuwan da suka haɗa da dabino 200, zogale 100, kashu 100, Magoro 50 Da kuma Guiba da sauran su, ga shugabar ƙungiyar, Ameerah Hajiya Khadeeja Aboubakar, inda ya yi bayanin cewa waɗannan itatuwan waƙafi ne da suka nema kuma aka bada da zimmar yin amfani da su da yadda ya da ce, kamar yadda suka nema, kana ya kara bayanin Muhimmancin, sirri da Alfanun da ke cikin Shukka itace a addinance, bangaren haɓaka tattalin arziki da magance gurgusowar Hamada.

Shugaban wanda ya samu wakilcin ɗaya daga cikin mataimakan sa Mukhtar A. Haliru Tambuwal.

Da ta ke karɓar Itacen shugabar ƙungiyar, Ameerah Hajiya Khadeeja Abubakar, ta yi godiya da bada tabbacin yin amfani da su kamar yadda suka buƙata.

Ta bayyana irin dadaddar alaƙar da ke tsakanin ƙungiyar da hukumar da sauran ƙungiyoyin addinin Musulunci a Sakkwato, ta bayyana irin taimakon da Gwamnatin jihar Sakkwato da mai martaba sarkin Musulmi ke yi masu don haɓaka lamurran ƙungiyar da na makarantar da suke kan ginawa ta jin kan marayu da mabuƙata.

Ta yi fatar Alheri da godiya ga dukkan waɗanda su ka yi faɗi ta shi har aka samu waɗannan itacen.

Kafin barowar wakilin Sadaukin Sakkwato sai da aka ƙaddamar da da sa wasu iraruwan a matsayin wakafi.

Wasu mambobin qungiyar sun yi godiya, an kuma gabatar da addu’a ta musamman akan wannan waƙafi da tawassulin Allah ya kawo mana jihar Sokoto Nijeriya da ma Nijar ƙarshen matsalolin da ke damun ƙasashen biyu baki ɗaya.