Ya kamata a gaggauta hukunta makasan Sheikh Aisami – JNI

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Ƙungiyar Jama’atul Nasril Islam (JNI) ta buƙaci Gwamnatin Tarayya da shugabannin sojoji da su gaggauta gurfanar da sojojin da ake zargi da kisan fitaccen malamin addinin Musuluncin nan na jihar Yobe, Sheikh Muhammad Goni Aisami.

Ƙungiyar ta JNI ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Litinin ta hannun Babban Sakatarenta, Dokta Khalid Abubakar Aliyu, inda ta ce, ba wai kawai a yanke hukuncin ba har ma da duba yadda aka yi kisan.

Ƙungiyar ta kuma ce ya kamata a yi amfani da irin hukuncin ga duk wani lamari makamancin haka a ƙasar nan, domin ya zama izina.

Sai dai ya ce, bai kamata a ci gaba da yin tashe-tashen hankulan da ake tafka wa a ƙasar ba yana mai cewa, “muna da tabbacin cewa waɗannan kashe-kashen da ba su dace ba, galibi an yi tunanin aikata su ne.

“Ƙungiyar JNI ta yi matuqar kaɗuwa da rahoton kisan da aka yi wa Sheikh Muhammad Goni Aisami tare da sace masa mota.

“A taƙaice dai, kisan Shehin Malamin abu ne mai ban tsoro, abin zargi, kuma abin Allah-wadai, idan aka yi la’akari da irin halin kirkin Malamin, wanda a ra’ayinsa ya bai wa maharan dama su hau mota ɗaya,” inji JNI.

A wani labarin kuma, Ƙungiyar Jama’atu Nasril Islam (JNI) ta yi Allah-wadai da matsayin da Ƙungiyar Kiristoci ta Nijeriya (CAN) reshen jihar Filato da wasu ƙungiyoyi suka ɗauka kan batun sake gina babbar kasuwar Jos.

JNI wacce ke ƙarƙashin jagorancin Sarkin Wase, Dokta Muhammad Sambo Haruna, a jihar ta Filato, ta bayyana haka ne a martaninta ga CAN din kan batun sake gina kasuwar.

An yi ta cece-kuce kan ko za a gina kasuwar ko kuma ba za a yi ba biyo bayan yarjejeniyar da Gwamnatin jihar ta ƙulla da Bankin Jaiz.

Yarjejeniyar, a cewar Gwamnatin jihar ita ce ta samar da kuɗin gudanar da aikin, lamarin da CAN ta ce ya kamata a dakatar da shi.

Ƙungiyar ta JNI a cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun Sakatarenta na Jihar, Salem Musa Umar, ta ce kalaman abun kyama ne da kuma tunzura al’ummar Musulmin jihar sannan kuma cin mutunci ne ga addinin Musulunci.

Sanarwar ta ce, “Babban abin da ya fi damun mu shi ne faifan bidiyo da ke yawo a kafafen sadarwa na zamani inda wani ke bayani a ƙarƙashin reshen wata ƙungiyar da ta kira kanta ta Masu Kishin Kiristoci ta Jihar Filato

“Muna mamakin tun yadda aikin sake gina babbar Kasuwar Jos ya koma batun addini, cewa ƙungiyoyin addini za su yi amfani da ita wajen jefa kalamai na cin zarafin Musulmi da Musulunci?” inji sanarwar.

Ƙungiyar JNI ta bayyana kaɗuwa da cewa wanda a cikin bidiyon ya bayyana Musulmi a matsayin ’yan ta’adda kuma ya zarge su da kona kasuwar a lokacin da ta ce rabin masu shaguna da masu gudanar da kasuwanci a ciki Musulmai ne.

JNI ta ce ta tsaya ba don kawai bankin Jaiz na da hannu a ciki ba, ta yi imani da inganci da buƙatuwar ganin babbar kasuwar ta dawo aiki domin amfanin kowa da kowa a jihar.