Juyayin kisan gilla ga Sheikh Aisami

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA

Dama kowace rai lalle wata rana za ta ɗanɗani mutuwa, barin duniya ko rabuwar gangar jiki da rai wajibi a rayuwar talikai.

Sanadiyyar mutuwa kan bambanta tsakanin masu rai. Wani kan yi doguwar jinya har a fidda rai, wani gajeruwar jinya, wani zai shiga ya rufe ne amma sai a wayi gari rai ya yi halinsa.

Akwai waɗanda kan gamu da ajali ta hanyar hatsarin mota ko wasu su samu harin ’yan ta’adda ta hanyar harbi da bindiga. Koma ta yaya lamarin ya faru duk hanya ce ta rabuwa da wannan ran da a ke yi wa kirari da ‘rai baƙon duniya’ don haka duk daɗewar da mai rai ya yi a doron ƙasa mutuwa na nan.

Shi ya sa duk masu dabara kan yawaita addu’ar gamawa da duniya lafiya. Kun ga duk abun da babu makawa sai ya afku to ai ba wata dabara kenan da ta wuce sakankancewa da hukuncin Allah ta hanyar rashin mamakin zuwan ta a kowane lokaci a kuma kowane irin hali.

Wannan shimfiɗa ce kan mutuwa don juyayin rashin shehun malamin Islama a Jihar Yobe Goni Aisami. Wasu kan rubuta sunan da ‘Gwani’ amma shi marigayin yak an rubuta sunan sa da ‘Goni’ don haka na zavi ɗaukar na marigayin ko ma a iya wannan rubutun ne.

An wayi gari a makwan jiya da labarin wani soja ya yi kisan gilla ga malamin a da ke dawowa gida daga Kano zuwa Gashua. Labarin ya nuna cewa marigayi shaharerren lamain ya ragewa sojan hanya ne zuwa garin Jajimaji da ke ƙaramar hukumar Karasuwa inda bayan ya tsaya don kama ruwa sojan ya yi ma sa barazana da bindiga a kan kar ya kuskura ya ƙaraso wajen motar inda malamin kuma cikin mamaki ya ƙaraso don dukiyarsa ce kuma bai yi wa sojan laifin komai ba hasalima taimakon sa ya yi ta hanyar rage ma sa hanya. Nan dai labari ya zo cewa sai ya buɗe masa wuta inda hakan ya yi sanadiyyar rasuwar malamin.

Sojan wanda majiyoyin ’yan sanda su ka bayyana sunansa da John Gebriel ya yi ƙoƙarin tada motar marigayin don awon gaba da ita don ba mamaki barawon mota ne sai motar ta ki tashi. Hakan ya saya kira abokinsa wanda shi ma soja ne mai suna Adamu Gideon don kawo ma sa ɗauki. Shi ma Gideon ya zo amma sai motarsa ta samu matsala. A taƙaice dai nan ’yan sanda su ka samu kira daga ’yan sintiri inda su ka zo su ka cafke jami’an sojan biyu.

Haƙiƙa kisan gillar ya ba da mamaki ainun don yadda a na zaton wuta a maƙera a ka samu a masaqa. Ma’ana a yanda a ka ɗauki jami’an tsaro masu aikin kare rayuka da dukiyoyin al’umma sai a ka samu wasu baragurbi a ciki da kan bata sunan su. Idan ka na tafiya a kan babbar hanya zaka so ka ga jami’an tsaro na tsaye su na kula da lamuran da ke faruwa sai ka ga hankalin mai tuƙa mota ya kwanta don ya san ko da ’yan fashi ne da masu satar mutane su ka zo aƙalla jami’an tsaro za su taɓuka wani abu wajen ba da kariya sai dai in abun ya fi ƙarfinsu.

Wata majiyar ma na nuna shehun malamin ya ɗauki marigayin ne daga wata madakatar motoci inda fahimtar soja ne ya sa cikin kwanciyar hankali ya amince ya ɗauke shi don ka taimakawa mai taimakon kare ran ka daga miyagun iri ai ba wani abu ne mai wahala ba. Ba ma wani sabon abu ne a madakatar motar jami’an tsaro su kan tsayar da masu mota su nemi su ragewa wasu daga cikin su hanya zuwa ƙauye na gaba ko madakatar mota ta gaba.

Wani lokacin ma jami’an tsaron kan buƙaci a ragewa wani farar hula hanya bayan kammala kai mu su ziyara a wajen binciken su zuwa gari na gaba ko ma gari mai nisan gaske da zai iya kai wa kilomita 150. Yawancin masu motoci musamman waɗanda ke tafiya ba tare da fasinja ba kan taimaka cikin farin ciki wajen ɗaukar jami’an da jama’ar su. Wani lokacin ma har da yin ihsani ga jami’an in an zo rabuwa.

Yanayin ya kan kai har ga ƙulla zumunci inda a kan yi musayar lamba da jami’an a na gaisawa lokaci-lokaci. Sai wannan karo Sheikh Aisami ya yi taimako inda hakan ya yi sanadiyyar ajalinsa. Rayuwa kenan ba wanda ya san ranar komawarsa. Wata nasara a nan ita ce yadda ba a juya maganar ba cewa wasu ’yan ta’adda ne su ka kashe malamin.

Gaskiya soja bai gwanance da ƙulle-ƙulle ba. Ka ga in da wasu baragurbin ne da sun nuna gudunmawa su ka kawowa malamin yayin da a ka kawo ma sa hari ko kuma su yi ƙoƙarin ingiza motar Gideon gaba ta bar daidai wajen da lamarin ya faru. Kazalika za su iya buɗe wa motar Gideon wuta don badda sawun abun da ya wakana. Zuwa da a ka yi a ka same su a wajen kuma a ka cafke su na nuna yiwuwar samun muguwar rana gare su.

Duk da haka ba mamaki in an tsananta bincike a gano ko hakan ma ya sha faruwa a baya da zai zama an yi kisa sai a ce ’yan ta’adda ne su ka kai hari. Yankin arewa maso gabar na daga yankuna da a baya su ka fi ko ina hatsari a Nijeriya. Zubar da jinin waɗanda ba su yi laifin komai ba ba wani sabon abu ba ne.

Afkuwar wannan babban akasin zai jefa tsoro a zuciyar mutane in su na bin manyan titunan Nijeriya kuma su ka tinkari yankuna masu hatsari. Mataki mai ƙarfi da kwatanta adalci shi ne kawai zai iya zama mafita ga wannan abun ban takaici da tsoro.

An ƙara yin wani dacen inda rundunar sojan Nijeriya ta bayyana amincewar ta ga yin aiki da ’yan sanda don gudanar da bincike kan sojojin da ke aiki a Nguru. Babbar matsalar da ke damun jami’an tsaro a Nijeriya ita ce rashin aiki tare wajen magance matsalolin tsaron ƙasa. A kan samu kowace runduna na yin aiki ne a gefen ta ba da sha’awar son haɗa kai da ’yar uwar ta ba don cimma nasara.

Alal misali wannan runduna za ta samu labari mai muhimmaci ga tsaron ƙasa amma ba za ta bayyana wa ’yar uwar aikin ta ba don ɗaukar mataki tare. Idan soja ya ga abun da ɗan sanda ya dace ya yi ya dace ya miqa ma sa bayani hakanan shi dan sanda in ya ga na ɓangaren soja. Hakanan sauran jami’an tsaro na farin kaya, shige da fice, kwastam da sauran su.

Haƙiƙa in dai a ka tsananta bincike kan wannan zalunci, za a iya samo bakin zaren rage afkuwar irin haka a gaba. Tun da na ga an kama sojojin ba tare da an ba da labarin samun hatsaniya tsakanin su da ’yan sanda ba, nace in Allah ya yarda za a gano gaskiyar lamarin. Ai ba baƙon abu ba ne a nemi musayar wuta tsakanin sojoji da ’yan sanda.

Ko sojoji su gayyato abokan aikin su a yi ta ɗauki ba daɗi tsakaninsu da ’yan sanda ko ma jama’ar gari. Ni kai na a wata shekara ina tuƙi a tsakiyar gari sojoji su ka taho da motarsu da gudu ɗaya daga cikin su ya sa kan bindiga ya huda marfin injin motar don cin zarafi na a matsayi na farar hula da ba ya ganin ina da wani amfani a ƙasa. Yawanci irin wannan akasi ya kan faru amma mutane kan yi Allah ya isa su bar maganar a nan.

Na taɓa ganin wani soja da a ka kama wanda ya ƙware wajen huda tayun motoci inda rannan ya shiga rikici da direbobin manyan motoci inda ya ɗana bindiga zai yi harbi sai mutanen suka yi ƙoƙarin hana shi. A sanadiyyar hakan hannun saya taɓa kunama ya kashe mutum biyu.

Kammalawa;

Shugaban ƙungiyar JIBWIS Sheikh Abdullahi Bala Lau ya buƙaci gwamnatin Nijeriya ta fitar da matsaya kan waɗanda a ke tuhuma da hannu a kisan gilla ga babban malamin nan na Islama a Yobe Sheikh Gwani Aisami.

Sheikh Bala Lau na magana ne bayan miƙa saƙon ta’aziyya ga iyalin marigayin wanda ke cikin manyan malaman ƙungiyar.

Imam Bala Lau ya ƙara da cewa, lamarin ya girgiza ƙungiyar don irin hanyar da marigayi Sheikh Aisami ya rasa ran sa daga bayanan da a ke bayyanawa na ragewa wani jami’in soja hanya zuwa Jajimaji a karamar hukumar Karasuwa da ke jihar Yobe.

Malamin na Islama ya jaddada cewa ɗaukar matakin yin adalci ga jinin marigayin shi zai karya lagon masu irin wannan ɗabi’a ta cin amana.

A nan Sheikh Bala Lau ya nuna takaicin yadda wake ɗaya ke neman vata miya a tsakanin jami’an soja waɗanda a ka sani da aikin kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

Marigayi Sheikh Gwani Aisami na gabatar da wa’azi da tallafa wa zaman lafiya a yankin da ke farfaɗowa daga illar Boko Haram.