Dalilinmu na umartar ɗalibai biyan Naira 1,000 bayan buɗe Kwalejin da Deborah ta yi ɓatanci ga Annabi – Shugaban Kwaleji, Dakta Hakimi

Daga AMINU AMANAWA SOKOTO

Shugaban Kwalejin Ilimi ta Shehu Shagari dake Sakkwato Dakta Muhammad Wadata Hakimi, Walin Wazirin Sakkwato ya bayyana dalilan da suka sanya hukumar gudanarwar makarantar sanya kowane ɗalibin kwalejin biyan Naira 1000 dama rattaba hannu kan cewa ba za su sake tayar da tarzoma a kwalejin ba, irin wacce aka samu a watannin baya. Shugaban ya dai bayyana hakan ne a tattaunawa ta musamman da wakilin Blueprint Manhaja na Sakkwato, Aminu Amanawa ya yi da shi a ofishinsa.

BLUEPRINT MANHAJA: Waɗanne irin matakai ne kwalejin nan ta bi kafin kai wa da sake buɗe kwalejin, biyo bayan irin tarzomar da aka samu a baya na kisan ɗalibar da ake zargi da ɓatanci ga fiyayyen halitta Annabi Muhammad SAW?
DAKTA HAKIMI: To Alhamdulillah, na ɗaya dai abinda muka fara yi shi ne, aiwatar da umarnin mai girma gwamna da ya bayar na cewa kwamitin su kira ganawa domin su tsara yadda za a buɗe makarantar. Mun yi taron ganawar da maigirma Gwamna ranar Talata, ranar Alhamis kuma muka yi wani taron, wanda ya ba da shawarwarin yadda za a yi.

Na farko dai aka yi ta roƙon a buɗe makaranta ranar litinin takwas ga wata, sannan kuma ɗalibai za su sa hannun rantsuwar cewa ba za su sake yin abubuwan da za su tayar da hankali ba da zai kawo irin matsalolin da suka kawo ba, wanda yake ya ƙunshi cikin sharuɗɗan ba wanda zai koma yin batanci da wani addini na Musulunci ko Kirista, kowa ya mutunta addinin wani, sannan kuma kowa ya zo nan ranar litinin ya sa hannu.

Ka san kuma dama kafin abinda ya faru ya faru, ana jarabawa ta ƙarshen zango na biyu, to sai muka bari a ba da sati biyu ɗalibai su shirya sai a cigaba da jarabawar da aka soma tunda farko.

Dukkannin ɗalibai ne za su rattaba hannu kan wannan kundin cewa ba za su sake tayar da tarzoma ba?
Eh, ɗalibai tun daga matakin neman takardar shedar malanta ta NCE zuwa masu karatun Digiri dukkan su ne za su rattaba hannu a wannan takardar.

Me ita wannan takardar ta ƙunsa ne?
Kawai ta ƙunshi cewa ni wane… mai karatu kaza… a mataki na kaza… na yi alƙawarin cewa ba zan sake sa kaina cikin wani abu da zai kawo tarzoma ko tashin hankali ba a cikin wannan Kwalejin ilimi ta Shehu Shagari, ko kuma ɓatanci ga wani addini. Idan kuma na yi, hukumar makaranta tana da damar ɗaukar duk hukuncin da ta ga dama a kaina bisa doka.

Baya ga wannan sa hannu, ko akwai wasu sharuɗɗa ko dokokin da kuka gindaya wa dalibban?
Babu wani wannan ne kawai.

Akwai bayanan dake yawo cewa ko wane dalibi sai ya biya N1000 kafin ci gaba da karatu. Ban sani ba ko hukumar makaranta ce ta fito da wannan?
A’a, kwamitin ne ya fito da wannan, kuma ka san lokacin da aka yi rikicin an koma ofishin jami’an tsaro na makaranta, kuma ɗalibai sun kona wasu motocinsu, to kaga kansu suka wa varna. To an sa wannan ne a matsayin ladabtarwa domin ya zama darasi saboda kowa zai ji a jikinsa, sannan kuma za a yi amfani da kuɗaɗen wajen gyara ofishin da ma motoci.

A tarihin kwalejin ilimi ta Shehu Shagari dake nan Sokoko ko an taɓa samun makamancin irin wannan rikicin?
Gaskiya ni dai a iya sani na rabon da a samu irin wannan tun a shekarar 1999 rabon mu da samun irin wannan matsalar, kodayake wannan ba sha’anin ɓatanci ga addini ba ne a wannan lokacin, ka ga wannan kuma ɓatanci ne. Kuma ba wanda zai yi haƙuri na irin wannan ga dukkan cikakken musulmi na vatanci ga fiyayyen halitta Annabi Muhammad S.A.W.

Wanne mataki hukumar wannan Kwalejin ke yi domin kauce wa sake faruwar irin abunda ya faru a baya?
Ƙwarai da gaske wannan dai kawai zuwan abu ne, dama akwai matakan domin akwai ma’aikatan DSS, SIB, duk suna ciki wasun su ma calibai ne a wannan kwalejin, kuma suna taimaka wa hukumar makaranta.

Kuma ka ga wancan abinda ya faru, sakon murya ne kuma shi cikin ƙanƙanin lokaci yake bazuwa a kafofin sada zumunta, kuma ko a lokacin mun samu bayanai inda muka kira DSS muka miƙa ta hannunsu, kuma a hannunsu ne ma ɗalibai suka hallaka ta.

Da yake za a dawo a cigaba da jarabawa, idan aka kamala za a je hutu ne ko kuma za a cigaba da wani zangon karatu ne?
Da ma a shirinmu za mu kamala a wancan lokaci ƙarshen watan Mayu. Kuma idan an ƙare, za a je dogon hutu da ba za a dawo ba sai watan Satumba. Amma ka ga yanzu ana sa ran kamala jarabawar a 8 ga watan Satumba, ka ga su kenan sun gaji da hutu, domin kafin a buɗe, su kansu sun yi ta kira da don Allah a sake buɗe wannan kwalejin, saboda haka, ba wani dogon hutu  za ta je ba.

A duk shekara na san wannan Kwalejin tana shirya bikin al’adu dake haɗa kan mabanbantan harsuna da addinai, ya batun yake a wannan shekarar?
Ai an rigaya ma da an yi na wannan shekarar, sassan karatu na ‘social studies, ‘Hausa’ da ma nazarin harshen turanci sun riga da sun gudanar da taron, mako ɗaya kafin soma jarabawar zangon karatu na biyu da aka samu wannan matsalar. Amma Insha’Allah za a cigaba.

Kamar adadin ɗalibai nawa ne ke karatu a wannan kwalejin?
Yanzu muna da sama da ɗalibai dubu 9,000 dake karatu duka a wannan kwalejin.

Harabar kwalejin

Daga ƙarshe, menene kiran ka  ga waɗannan ɗalibban?
Eh, to kamar yanda kowa ya sani, makarantarmu ta yi suna sosai wajen son zama lafiya da kwanciyar hankali da waɗanda ba yare ɗaya ko addini ɗaya ba. Idan ka lura ko waɗanda ba ‘yan asalin Sakkwato ba N4,500 ne suke biya duk shekara na muhallin kwana, muke ba su ruwan sha da wutar lantarki, ka ga kenan, waɗanda suka baƙunce mu ne basu kyauta mana ba. Duk wannan hidimar a ce ka yi ɓatanci ga addinin galibin mutanen wurin.

To, za mu cigba da zama da wanda zai bi dokokin makaranta da zai mutunta mutuncinmu dana addinin mu, domin wannan kwalejin Najeriya ce gabaɗaya. A nan, ba ɗan jihar da babu, ƙabila, dama yare. Kuma shekarunmu 52 muna wannan aikin, ɗalibanmu sun yi fice a fannoni daban-daban na rayuwa. Don haka, mu na kira ga ɗalibai da su kasance masu bin dokokin makaranta da mutunta abokanin zama.

Idan ma matsaloli sun faru, a sanar mana domin ɗaukar matakin da ya kamata a ce an ɗauka. A ɓangaren gwamnati kuwa, mu na kira gare ta da a yi dokoki masu kyau da za su hana irin waɗannan abubuwan faruwa.