Garkuwa: Bayan mako uku ’yan sandan Zamfara sun ceto wasu mata

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Rundunar ‘yan sandan Jihar Zamfara ta ceto wasu mata biyu da wasu ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su a ƙaramar hukumar Bungudu da ke jihar.

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan SP Muhammad Shehu ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai ranar Litinin.

“A ranar 20 ga watan Agusta, 2022, jami’an rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara yayin da suke sintiri tare da Nya Mango a ƙaramar hukumar Bungudu, sun ɗauki matakin ceto wasu mata biyu da aka yi garkuwa da su ba tare da wani sharaɗi ba, wato Ubaida Hassan, ‘yar shekara 12, tsohuwa da Umaima Jamilu ‘yar shekara 10 a qauyen Gidan Liman da ke gundumar Kekun Waje a ƙaramar hukumar Bungudu.”

A cewarsa, ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda ɗauke da makamai sun sace waɗanda aka ceto a ranar 15 ga Yuli, 2022 bayan harin da aka kai ƙauyen.

“An duba lafiyar waɗanda abin ya shafa a babban asibitin Bungudu, daga nan kuma ‘yan sanda sun tantance su sannan aka miƙa su ga iyalansu,” ya ce.

 Rundunar a yayin da ta ke tabbatar wa jama’a da himma wajen kare rayuka da dukiyoyi.

Shehu ya ce rundunar ta buƙaci kowa da kowa da su kasance masu lura da tsaro kuma su kai rahoto ga ‘yan sanda ko duk wata hukumar tsaro domin ɗaukar matakin gaggawa.