Sojoji sun halaka ‘yan bindiga 19 a Jihar Kano

Spread the love

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Sojojin Nijeriya, ƙarƙashin rundunar sintirin haɗin gwiwa, MESA, ƙarƙashin bataliya ta uku, sun fatattaki harin da ƴan ta’adda su ka kai kan al’ummomi a ƙaramar hukumar Shanono ta Jihar Kano, inda suka kashe mutane 19 daga cikin maharan.

Kazalika, majiyoyin sun nuna cewa sojojin, tare da haɗin gwiwar wasu jami’o’in tsaro, sun yi artabu da ƴan bindigar bayan samun bayanan sirri game da motsinsu a yankunan Ungwan Tudu, Ungwan Tsamiya, da Goron Dutse, misalin ƙarfe 5:00 na yamma, ranar 1 ga Nuwamba, 2025.

A cewar wata sanarwa da Kyaftin Babatunde Zubairu, mataimakin daraktan hulɗa da jama’a na sojoji na bataliya ta 3, ya fitar, sojojin sun gaggauta fita don daƙile harin, inda suka yi wa ‘yan bindigar kwanton ɓauna yayin da suke wucewa akan babura, inda akai bata-kashi.

“A yayin fafatawar, an kashe ‘yan bindiga 19 yayin da aka ƙwato babura da dama da kuma wayoyi guda biyu daga hannun su,” in ji sanarwar.

Sanarwar ta ƙara da cewa, sojoji biyu da ɗan sa-kai guda ɗaya sun rasa rayukansu a yayin yakin.

Kyaftin Zubairu ya ce, ana ci gaba da gudanar da ayyukan sintiri a yankin domin kare al’ummomin da ke cikin zaman ɗar-ɗar, waɗanda aka daɗe ana kai wa hare-hare da satar shanu da sauran laifuffuka.

By ukarofi