Sojoji sun kashe ’yan ta’adda 82 a Zamfara

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Hedikwatar Tsaro (DHQ) a ranar Alhamis, ta bayyana cewa, wani farmakin da rundunar sojin sama ta ‘Operation HADARIN DAJI’ ta kai ta sama ta kashe ’yan ta’adda aƙalla 82 yayin da wasu da dama suka samu raunuka daban-daban a ƙauyen Ƙofar Ɗanya da ke ƙaramar hukumar Bukkuyum a Jihar Zamfara.

Rundunar sojin ta kuma ce, an kama ɓarayin mai 26 da dakarun ‘Operation DAKATAR DA BARAWO’ da ‘OCTOPUS GRIP’ suka kama a yankin Neja Delta na ƙasar nan.

Daraktan ayyukan yaɗa labarai na tsaro, Manjo Janar Benard Onyeuko ne ya bayyana haka a lokacin da ya ke yiwa manema labarai ƙarin haske kan nasarorin da sojoji daban-daban suka samu a lasar daga ranar 16 zuwa 30 ga watan Yunin 2022.

“Bayan rahoton harin da aka shirya kai wa ƙauyen Ƙofar Ɗanya, rundunar sojin sama ta yi tattaki zuwa wurin, inda ta hango ’yan ta’adda sama da ɗari da hamsin (150) sun taru a tsakiyar ciyayi.

“A bisa ga haka, tawagar rundunar sojojin saman Nijeriya sun yi taho-mu-gama da ’yan ta’addar da bama-bamai da suka lalata sansanin ‘yan ta’addan. A saboda haka, sahihan bayanai daga mazauna yankin Ƙofar Danya sun bayyana cewa sama da tamanin da biyu daga cikin ’yan ta’addar sun samu munanan raunuka inda aka kashe da yawa daga cikinsu yayin da wasu kuma suka samu raunuka daban-daban,” inji shi.

Da ya ke ƙarin haske game da ayyuka a shiyyar Kudu maso Kudu, Onyeuko ya ce, sojojin sun ƙwato ɗanyen mai na sata, ƙwale-ƙwalen katako 68 da jiragen ruwa masu sauri 9 da dai sauran kayan aiki daga masu zagon ƙasa.

“Jimillar lita miliyan uku da dubu saba’in da huɗu (3,074,000) na Man Fetur, miliyan uku da ɗari takwas sannan dubu uku (3,810,000) na ɗanyen mai, lita dubu goma sha huɗu (14,000) na fetur, sannan an gano lita biyu na kalanzir,” inji shi.