Ansaru ta haramta harkokin siyasa a Birnin Gwari

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Ƙungiyar Ansaru ta haramta duk wasu harkoki da ke da alaqa da siyasa a yankin Ƙaramar Hukumar Birnin Gwari ta Jihar Kaduna.

Ƙungiyar cigaban masarautar yankin ta ce, yanzu haka ƙungiyar ta shimfiɗa wasu sharuɗɗa da suka dace da salon shugabancinta, kuma duk wanda aka samu da saɓa su, yana iya fuskantar hukunci mai tsanani.

Bayanan da BBC ta tattara sun bayyana cewa, ƙungiyar ta raba wa jama’a wani saƙo da ke ƙunshe da dukkan manufofinta, ciki har da na kawo ƙarshe tsarin dimukraɗiyya da kuma harkokin siyasa a yankin bakiɗaya.

A yanzu dai mutanen garuruwan da dokar ta shafa, kan saci jiki zuwa wasu wuraren ne don gudanar da tarukan siyasa a duk lokacin da buƙatar hakan ta taso.

Ko a makon da ya gabata ma an yi baikon wasu mayaƙan ƙungiyar da mata biyu, kuma tun kafin auren da ake sa ran ɗaurawa ranar Asabar mai zuwa, sun shaida wa iyayensu cewa za su zauna da su ne a can daji, kuma ka da a kai su da kayan ɗaki, wato kujeru da sauran kayan alatu, face katifa kawai da ‘yan kwanukan abinci.

Wani abun tayar da hankali da ke faruwa a cewar shugaban ƙungiyar cigaban yankin na Birin Gwari Malam Ishaq Uman Kasai, shi ne yadda matasa ke rungumar manufofin ƙungiyar suna shiga.

BBC ta tuntuɓi kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na Nihar Kadunan Samuel Aruwan, sai dai haƙa ba ta cimma ruwa ba.

Jihar Kaduna dai na daga cikin jihohin Nijeriya da suka fi fama da matsalar tsaro a halin da ake ciki, inda ‘yan fashin daji da sauran ƙungiyoyin masu iƙirarin jihadi ke cin karensu babu babbaka.

Lasar takobin shawo kan irin waɗannan matsaloli da mahukunta ke yi a Nijeriya ba sabon abu ba ne, sai dai mazauna irin waɗannan wurare na ƙorafin cewa har yanzu dai jiya i yau.