Sojojin Nijar sun damƙe ƙasurgumin ɗan bindigar Nijeriya, Kachalla Ɓaleri

Daga UMAR GARBA a Katsina

Ɓaleri, wanda tun da farko ya tsere daga hannun sojojin Jamhuriyar Nijar, da ake kira ‘Operation Farautar Bushiya,’ sun kama shi a ranar Talata a unguwar Rouga Kowa Gwani da ke garin Guidan Roumdji.

Da yake tabbatar da kamun ɗan bindigar, Babban Hafsan Rundunar Operation Faraoutar Bushiya, Kanar Mohamed Niandou, ya ce an kawo ƙarshen mulkin Ɓaleri a ranar Talata yayin da yake ganawa da mutanensa domin shirya kai hare-hare a Nijeriya da Nijar.

“Gwamnan yankin, CGP Issoufou Mamane, da mai shigar da ƙara na ƙasar, Adamou Abdou Adam, sun yaba da ƙwarewa da jajircewar sojojin da aka tura aiki a taron gabatar da masu aikata laifuka da aka shirya.

Sanarwar ta ce, “Sun ce kamun babbar nasara ce a yaƙin da ake yi da ‘yan bindiga da kuma ta’addanci a yankin,” in ji sanarwar.

Jaridar PRNigeria ta ruwaito cewa, Ɓaleri ɗan asalin garin Shinkafi ne a jihar Zamfara wanda ya yi ƙaurin suna wajen addabar mazauna yankin Arewa maso Yamma da suka haɗa da Katsina da Zamfara da Sokoto da Maraɗi a jamhuriyar Nijar.

Ana alaƙanta shi da sace-sacen mutane da kuma kashe-kashen jama’a a yankin Arewa maso Yamma.

A makonnin da suka gabata ya fitar da wani faifan bidiyo inda ya nuna tarin takardun Naira da ake zargin kuɗaɗen da ake karɓa a matsayin kudin fansa ne daga ayyukan sace-sacen tawagarsa.