Taɓarɓarewar tarbiyya da zumunci suna ba ni tsoro – Alƙali Nazir Abdullahi 

“Alƙalanci na buƙatar isasshen lokaci, nazari da bincike”

Daga BUSHIRA NAKURA 

Alƙali Naziru Abdullahi Tamburawa ya bayyana baƙin ciki da takaicinsa bisa yadda tarbiyya da kuma zumunci a yau suka lalace har ta kai ga ba shi tsoro, saboda taraddadi da zulumun halin da al’umma za ta iya tsintar kanta a ciki, idan har aka ci gaba da tafiya a haka. Mai shari’a Naziru Tamburawa dai ya bayyana hakan ne a lokacin da yake tattaunawa da Wakikiyar Blueprint Manhaja, BUSHIRA NAKURA. Ga cikakkiyar hirar tasu kamar haka:

MANHAJA: Mai karatu zai so jin cikakken sunanka, da inkiyarka da kuma taƙaitaccen tarihin rayuwarka.

MAI SHARI’A NAZIRU: Assalamu alaikum. Asalin sunana Naziru Abdullahi Tamburawa, inkiyata da ‘yan ajinmu a jami’a suke kirana da ita ita ce Kwamandan. An haife ni a garin Tamburawa a ƙaramar Hukumar Dawakin Kudu a shekarar 1982. Na taso a gidan makaranta, don haka na yi karatun allo a wajan ƙannen mahaifina Malam Mahdi Ma’aruf Liman, da kuma Malam Yahaya Ma’aruf, inda na kai izu arba’in sannan na tafi Goron-dutse gidan Sheikh Ashiru Shu’aibu, limamin Masallacin Khalifa Ishaƙa Rabi’u inda na ƙarasa hadda, sannan na yi juye, na yi tilawa har na hardace Alƙur’ani Mai tsarki. Wannann ɓangaren karatun allo ke nan. 

A ɓangaren karatun islamiyya kuwa na yi makarantar gidanmu ne mai suna ‘Nuruddin Islamiyya’, inda na karanta littattafai da dama kama daga na fiƙihu, hadisi, tarihi da kuma luggar Larabci. A sashin karatun boko kuwa, na yi ‘Tamburawa Yamma Primary School’. Daga nan kuma sai na tafi ‘G A S S Dawakin Kudu’. Kana na dawo cikin garin Kano da karatun nawa, inda na shiga ‘H I S Shahucci (Aliya).’ Daga nan kuma na tafi makarantar ‘Aminu Kano College of Islamic And legal Studies.’ Wato makarantar koyon shari’a da ke nan Gadon ƙaya a birnin Kano. Daga nan ne kuma na zarce Jami’ar Bayero (Bayero Uniɓersity Kano) don yin ilimi mai zurfi a fagen na shari’a. Yanzu haka kuma ni alƙali ne a ma’aikatar shari’a ta Jihar Kano.

To bayan aikin gwamnati da kake yi a ma’aikatar ta shari’a, kana wata sana’ar ne?

Aikin alƙalanci na buƙatar isasshen lokaci ne, da kuma nazari da bincike, don haka mai yin sa ba shi da lokacin da zai raba ƙafa, musamman ma duba da tarin shari’un da suke gaban kotuna a wannan ƙasa. Amma a baya dai na yi ƙananan sana’o’i da dama, saboda na yi tallan mangwaro, haka na yi tallan kifi, wannan tallan dukka na yi su ne bayan mun tashi daga karatun safe a wajan mahaifina limamin Tamburawa Sheikh Abdullahi Ma’aruf. Da na dawo cikin garin Kano kuma na yi sana’ar siyar da shadda a kantin kwari.

Ka na da aure? Idan ka na da shi, yaranka nawa?

Ina da aure mata ɗaya da ‘ya’ya huɗu, namiji ɗaya mata uku.

Ko za ka iya faɗa mana irin gwagwarmayar da ka sha a rayuwa?

Na sha gwamarmaya da yawa. Ina ɗaukar kifi a faranti in ta zagayawa. Haka wajan sayar da mangwaro ina tahowa da shi tun daga ƙauyanmu in sauka gidan rediyon Kano, in ɗauke shi a ka in shigo Railway, Sabon Gari, Fagge, Kantin Kwari har sai na siyar.

Bayam gwagwarmayar talla don neman na rufawa kai asiri, na yi gwamarmaya a ƙungiyoyi kamar Gizago Club, Burin zuciya, Youths Mobilization, Mu Gudu Tare Mu Tsira tare, Young Lerner’s. Da dai sauransu.

To a ɓangaren tafiye-tafiye, ƙasashe nawa ka taɓa zuwa, sannan a cikin gida jahohi nawa ka ziyarta?

To na dai taɓa zuwa jamhuriyar Nijar. A cikin gida Najeriya kuwa na je jahohi da dama, daga cikinsu akwai: Jihar Jigawa, da Jihar Katsina, da Jihar Zamfara, da Jihar Sokoto, da Jihar Kaduna, Benieu, Platue, Nassarawa, kogi, Edo. Da sauransu.

Ko akwai ƙasar da kake son zuwa idan hali ya samu?

Ina so na je Saudiyya (Makka da Madinah). Masar, ƙatar, Iraƙi, England da sauransu.

Ya kake kallon rayuwar da da ta yanzu?

Rayuwar da akwai sauƙi, ga zumunci, ga dattaku ko ba karatu da yawa akwai aiki da shi. Amma rayuwar yanzu ba sauƙi, ba zumunci, ba tarbiyya, haka kuma yanzu akwai tarin karatu amma ba aiki da shi.

Ko ka na da wani buri da kake son cikawa?

Burina shi ne samar da makarantar Islamiyya mai inganci da makarantar kimiyya da fasaha, da asibiti mai inganci musamman ɓangaran haihuwa.

Wacce shawara za ka ba wa mutane da kuma shugabanni?

Ina kira ga mutane su tashi su nemi na kansu, kada su zama bayi ga azzalumai su ringa amfani da su wajan jagaliyanci, mu duba tsarin kasuwanci irin na Inyamurai.

Wanne abu ne na farin cikin da ba za ka taɓa mantawa da shi ba?

Abin farin cikin da ba zan taɓa mantawa ba shi ne, yabo da mahaifiya ta ke yawan yi min kamar yadda ƙawayanta suke yawan gaya mini.

Wanne abu ne na baƙin ciki wanda ba za ka taɓa mantawa da shi ba?

Baƙin cikin da ban taɓa mantawa ba shi ne, muna shekara ta uku a jami’a zan shiga ‘lecture’ aka kira ni aka ce mahaifiyata ta mutu.

Mene ne yake ba ka tsoro a rayuwa?

Taɓarɓarewar tarbiyya da zumunci naa ba ni tsoro a wannan rayuwa.

Me ka fi so a yi maka kyauta da shi?

Na fi so a ba ni kyautar Alƙur’ani mai girma.

Wanne abu ne yake saurin saka ka jin haushi?

Abin da ya fi ba ni haushi shi ne cin amana.

Wanne abinci da abin sha ka fi so?

Na fi son tuwo miyar kuka da nama ko shinkafa da miya da nama. 

Yanayin gari, wanne ka fi so tsakanin damina da sanyi da zafi?

Na fi son yanayin damina.

Meye burinka wanda kake son cikawa?

Burin da nake so shi ne, na cika da imani.

Me ka fi so ga mutane?

Ina son mutane su nemi lahira uwa yanzu za su mutu, su nemi duniya kamar ba za su mutu ba.

Ko akwai abinda kake son cewa wanda ya shafe ka ko al’umma wanda ba a tambaye ka ba?

Abinda ba a tambaye ni ba ina so al’umar Arewa su san me suke yi a harkar tsaro, harkar lafiya da harkokin karatu da kasuwanci.

Su waye gwanayenka a duniya?

Gwanina Shugaban Halitta Annabi Sallallahu alaihi Wasallama. Ina son duk masu taimaka wa al’umma.

Wacce nasiha za ka yi wa matasa, musamman cima zaune wanda ba su son nema?

Kirana gare su shi ne, su tashi su nemi na kansu, saboda ko kaɗan zaman banza ba shi da rana face nadama da kuma da-na-sani.

Ka taɓa tunanin za ka zama ɗaya daga cikin alƙalai?

Ban taɓa zata ba a baya kafin na yi karatun shari’a.

Lokacin da aka rantsar da ku, me ya soma zuwa ranka?

Lokacin da ake rantsar da mu sai na ji kamar ba a kan ƙafata nake ba.

Ta wacce irin hanya kake ganin za ka iya taimaka wa al’umma da wannan aikin naka?

Zan taimaka wa al’umma da gaskiya da adalci in sha Allah.

Ka na ji a ranka cewar dama ba ka zama alƙali ba?

Gaskiya ba na ji, sai dai ina roƙon Allah kan aikata daidai.

Ko ka na da wanda za ka gaisar?

Ina gaisuwa ga dukkan masoyana da iyalina.

Mene ne fatanka ga Blueprint Manhaja?

Ina yi wa Blueprint Manhaja fatan alheri da ɗaukaka da ma’aikatanta.