Ta ya ake iya gane namiji na ɗauke da ciwon sanyi?

Daga AISHA ASAS

Mai karatu barkanmu da sake ganin zagayowar sati lafiya. Har wayau dai muna nan kan maudu’in namu na ciwon sanyi. Idan kana tare da mu, darasin namu ya soma ne tun daga ma’anar ciwon sanyi, yadda yake samuwa, yadda ake iya kaucewa samuwar shi, wasu ɗabi’u da muke yi da ke kai mu ga ciwon, matsayin sanya kayan ƙamshi a farji, alaƙar kayan mata da ciwon sanyi, da sauransu.

A wannan makon, shafin Kwalliya na jaridar Blueprint Manhaja zai waiwayi maza a matsala ta ciwon sanyi, na sani da yawa za su ji wannan darasi a matsayin susa a inda yake yi masu ƙaiƙayi, dalili kuwa shi ne, ciwon sanyi ya jima yana haddasa husuma tsakanin mace da namiji, inda kowanne daga cikinsu kan barranta kansa da ciwon, yana mai zargin ɗayan da kawo masa shi.

Duk da cewa ilimin ciwon sanyi ya wanzu ga al’umma, sai dai har zuwa yanzu ana samun waɗanda ke masa mummunan fahimta. A cewar wasu ana samun ciwon sanyi ne kawai a yayin samuwar aure, wanda hakan ke sa idan aka aurar da budurwa, ya kasance tana da ciwon sanyi sai a zarge ta da yin lalata, wanda a darussan da muka yi baya za mu iya ƙaryata wannan zancen.

Idan kun koma kan darasin namu na yau, wato ko ana iya gane ciwon sanyi a jikin namiji? Tabbas maza ma kan iya samun wasu daga cikin nau’ukan ciwon sanyi, kamar irinsu, Syphilis da Gonorrhoea, waɗanda zai iya ɗaukan su ne daga jikin mace, kuma zai iya yaɗa ciwon ga wata macen da ba ta da shi. Sai dai inda ruɗanin yake shi ne, ba a cika samun bayyanar alamomin ciwon ga jikin namiji ba kamar yadda suke bayyana a jikin mace. Wannan ne zai sa mazan musatawa idan matan suka tuhume su da hakan.

Bincike ya nuna cewa, ciwon sanyi da ke yawo tsakanin namiji da mata, ma’ana wanda namiji zai ɗauko ya sanya wa wata macen na da kaso mai yawa a matan da ke fama da matsalar ta ciwon sanyi, don haka yake da matuƙar muhimmanci ga shi namijin ya dinga lura sosai da irin wannan matuƙar yana da mace fiye da ɗaya. Saboda duk yadda ɗaya ta kiyaye kanta, idan ɗaya daga sauran matan ba ta yi ba, har ta kamu da cutar, dukka matan za su same shi matuƙar kana tarayya da su, anan kuwa kaga cutarwa ta shigo ciki.