Za a iya amfani da Zakkat da Waƙafi a yaƙi da talauci a Nijeriya – AZAWON

Daga MUKHTAR A. HALLIRU TAMBUWAL a Dutse

Shugaban ƙungiyar Hukumomi da ƙungiyoyin da ke aikin tattara Zakka da Waƙafi a Nijeriya, AZAWON, Malam Muhammad Lawal Maidoki, ya bayyana cewa, matuƙar za a yi amfani da kuɗaɗen da ake tattarawa daga Zakka da Waƙafi da sadakoki da masu hannu da shuni ke fitarwa, domin yaƙi da talauci, yunwa, da ƙuncin rayuwa da ake fuskanta a ƙasar nan.

Malam Muhimmad Lawal Maidoki (Sadaukin Sokoto) ya bayyana haka ne a yayin ƙaddamar da fara babban taron haɗaɗɗiyar ƙungiyar AZAWON ta ƙasa karo na 3, a garin Dutse, Babban Birnin Jihar Jigawa.

A cewarsa, duniya ta amince kan cewa fitar da Zakka da Waƙafi da musulmi ke yi wata hanya ce ta yaƙar talauci a tsakanin al’umma, wanda yake matsayin ƙudiri na 11 daga cikin ƙudirorin Majalisar Ɗinkin Duniya 17 na samar da cigaban rayuwa.

Malam Muhammad lawal Maidoki wanda har wa yau shi ne Mataimakin Babban Sakataren Majalisar Zakka da Waƙafi ta Duniya, ya bayyana cewa, ‘Wannan Babban Taro ya zo a lokacin da ya dace, daidai lokacin da rayuwar talakan Nijeriya ke fuskantar tsanani da hauhawar farashin kayan kayan masarufi.’

A yayin da farashin Dalar Amurka ke ƙara hauhawa a kasuwar bayan fage, inda Dala ɗaya ta haura Naira dubu ɗaya. Duk kuwa da yadda ƙididdiga ke nuna hauhawar farashin kayan abinci da na masarufi da ya yi tashin fiye da kashi talatin cikin ɗari na tsadar rayuwa, tun daga watan Satumba.

“Zan so na nemi tallafin gwamnatocin jihohi domin ɗaukar nauyin horar da matasa dubu game da dabarun aikin tattara Zakka da Waƙafi, tare da haɗin gwiwar ƙungiyar AZAWON.”

“Ina kuma ƙarfafa gwiwar gwamnatocin jihohi su samar da filaye masu faɗin kadada 100-500, domin noman rani wanda zai taimaka wajen samar da kuɗaɗen shiga da za a yi amfani da su wajen kula da marayu da marasa galihu.”

Ya ce, AZAWON tana ƙoƙari wajen ganin an yi amfani da tsarin tattara Zakka da Waƙafi a Nijeriya yadda zai dace da na sauran ƙasashen duniya, domin a ƙara ƙarfafawa da inganta tsarin. Wannan shi ne ya sa ƙungiyar ke ƙoƙarin haɗa kai da dukkan masu ruwa da tsaki a Nijeriya.

Shugaban ƙungiyar ya kuma buƙaci Gwamnatin Jihar Jigawa ta tallafawa reshen ƙungiyar da ke jihar, don su samu sauƙin gudanar da ayyukansu.

Wakilin Sarkin Musulmi kuma Uban Taro Sarkin Haɗejia Alhaji Adamu Abubakar Maje CON, ya roƙi al’ummar Musulmi da su fitar da Zakka kuma su bada Waƙafi ga masu hali, domin su tsarkake dukiyarsu, wanda yake umurni ne na mahaliccinsu.

Taron ya samu halartar ɗaukacin sarakunan gargajiya na Jihar Jigawa, shugabannin rassan ƙungiyar daga jihohi daban-daban, da wakilan Hukumomi da Ƙungiyoyin kula da tattara Zakka da Waƙafi daga jihohi, inda za a tattauna da gabatar da ƙasidu akan al’amuran da suka shafi karva da raba Zakka. Ana sa ran halartar wasu da za su gabatar da jawabai daga wasu ƙasashen duniya ta manhajar Zoom.