Mutanen Tudun Biri sun yi shahada, in ji Shugaba Tinubu

Spread the love

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sake nuna baƙin cikin sa kan harin bom da ya kashe mutane a garin Tudun Biri. Ya kuma yi wa mamatan fatan samun shahada.

Da yake jawabi a Masarautar Maiduguri a ziyarar da ya kai Jahar borno don halartar taron Chief of Army Staff Conference a yau litinin Shugaban ya ce:

“Har yanzu ina ƙara jaddada mana ta’aziyya kan asarar rayukan da muka yi a Kaduna, abin babu dadi Sam, amma a matsayin mu na mutanen da suka yi imani da ƙaddara dole mu karɓi wannan lamari a matsayin ƙaddara, sannan mu jajirce wajen ɗaukan matakan hana sake aukuwar hakan.

“Mutanen nan fa taruwa suka yi don su raya daren haihuwar fiyayyen Halitta Sallallahu Alaihi Wasallam ba don su illata kowa ba. Ka ga kuwa ai sun sami Shahada,” in ji Shugaban.

By Editor