Sarkin Katsina bai kori shirin AGILE a jihar ba

Daga UMAR GARBA a Katsina

A ƙarshen makon da ya gabata wasu kafafen yaɗa labarai sun ruwaito cewar, Mai Martaba Sarkin arkin Katsina, Alhaji Abdulmumin Kabir Usman, ya kori shirin nan da ke inganta ilimin ‘ya’ya mata wato AGILE a taƙaice, a wasu jihohin ƙasar nan ciki har da jihar Katsina.

Lamarin ya jawo cece-kuce musamman a kafafen sada zumunta bayan da wani babban malami da wasu jama’ar arewacin ƙasar nan suka zargi shirin da lalata tarbiyyar ‘yan mata ta hanyar koya masu wasu ɗabi’u da ka iya sa ‘yan matan su bijire wa addini da ma al’ada.

Sarkin labarai na masarautar Katsina, Malam Ibrahim Bindawa, ya musanta rahotannin, sai dai ya ce Mai Martaba Sarki ya kira taro don tattaunawa dangane da shirin inda ya gana da masu tafiyar da shirin a jihar da malamai da kuma sauran al’uma dake da ruwa da tsaki a shirin.

Ya ƙara da cewa, shi da kan shi ya rarraba takardun gayyatar taron tattaunawar, amma dai babu inda masarauta ta ce ta kori shirin AGILE daga jihar ta Katsina.

Kazalika, shugaban shirin a jihar Katsina ya ce ba su da wata masaniya ta korar shirin daga masarauta ko kuma daga gwamnatin Jihar Katsina, hasali ma ita gwamnatin jihar ce ke da alhakin kula da shirin ba masarauta ba.

Da yake mayar da martani kan lamarin, babban jami’in shirin a jihar, Dakta Mustapha Shehu, ya bayyana cewa, “Babu wani tsari da shirin ya zo da shi wanda za a ce ya saɓa wa addini zargi ne kawai waɗanda ba su facimci shirin ba ke yi.”

Ya ce, ba ‘yan mata ba ne kawai ke amfana da shirin har da maza, sai dai sun fi mayar da hankalin kan mata saboda su ne ƙididdigar da suka gudanar ta nuna ba sa zuwa makaranta kamar sauran takwarorinsu maza.

Da yake mayar da martani game da zargin shirin na ɓata tarayyar mata a jihohin Arewa ya ce, jihohi 19 ne ake aiwatar da shirin ciki har da na kudancin ƙasar.

Ya kuma ce, shirin ya tallafa wa makarantu 578 da miliyoyin kuɗi don a gyara su, yanzu haka kuma za a gina wasu sabbin makarantu 155 a ƙarƙashin shirin a jihar, ana kuma ba wa ɗalibai mata tallafin kuɗi waɗanda iyayensu suka amince za su bar su, su ci gaba da karatu daga matakin Firamare zuwa ƙaramar Sakandare har zuwa babbar Sakandare gami da ba su horon sana’a don dogaro da kansu, ana kuma koya masu yadda za su kai ƙara idan sun fuskanci cin zarafi da kuma yadda za su kare kansu a makarantu yayin da aka kawo musu hari.

“Babu wani tsari da shirin ya zo da shi wanda za a ce ya saɓa wa addini, zargi ne waɗanda ba su fahimci shirin ba ke yi,” inji shi.

Shehu ya kuma ce sarakuna, malamai da kuma masu unguwanni na sane da shirin saboda su ne ake ba wa kuɗi don su aiwatar da aiyukan da al’umar suke buƙata a ƙarƙashin shirin na inganta ilimin ‘ya’ya mata.