CBN ya dakatar da cajin da bankuna kan yi wa kostomomi yayin ajiyar kuɗaɗe

Daga BASHIR ISAH

Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya dakatar da harajin da akan karɓa yayin da kostomomi suka kai kuɗi mai yawa ajiya a banki.

Hakan na ƙunshe ne cikin sanarwar da Muƙaddashin Daraktan Sanya Ido, Dr Adetona Adedeji, ya fitar a ranar Litinin.

“Dukkanin bankunan da ke ƙarƙashin kulawar CBN su ci gaba da karɓar ajiyar kostomominsu ba tare da sun caje su komai ba,” in ji CBN.

Bankin ya kuma buƙaci bankuna da su bi wannan umarnin nasa sau da ƙafa.

Sanarwar ta ce sabuwar dokar da aka samar a Disamban 2019, mai lamba FPR/DIR/GEN/CIR/07/042, ita ce ta wajabta biyan haraji ga duk ajiyar kuɗi sama da N500,000 ga ɗaiɗaikun jama’a, sannan N3,000,000 ga hukumomi.

Sai dai, CBN ya ce a yanzu ya dakatar da tsarin biyan wannan haraji.

Ya ƙara da cewa dakatarwar za ta ci gaba da aiki har zuwa 30 ga Afrilun 2024.

A shekarar 2019 CBN ya bayyana cewa kostomomi su fara biyan haraji a duk lokacin da suka kai ajiyar kuɗi banki da ma cire kuɗi da zummar rage yawan tsabar kuɗin da ke karakaina a hannun jama’a.