Dandalin shawara: Ina neman dabarun da saurayina zai dinga ba ni kuɗi ko ba yawa

Daga AISHA ASAS 

TAMBAYA:

Assalamu alaikum. Aunty Aysha, ya ki ke? Ya yara? Don Allah shawara na ke so a ba ni. Ina da saurayi, yana so na, ni ma kuma Ina son shi, ga shi iyaye na sun matsa min akan na fito da miji nai aure. Ni kuma na kasa gaya mai yanzu haka wancan sati akai auren ƙanwata yanzu sun ce in ban fito da miji nan da wata ɗaya ba, duk wanda suka zaɓa min shi zan aura.

Ni kuma Ina son wancan, amma na kasa gaya mai, kuma shi wanda nake so bai ban kosisin kuɗi, bai tava haɗa ni da shi ba, shi ne nake so a bani shawara ta ina zan fara mai magana ya turo gidanmu, kuma aunty ko akwai wasu dabaru namu da za a gaya min yadda zai ɗan dinga ba ni kuɗi ko ba yawa.

Dan wallahi gidanmu har gori ake min wai saurayi na bai ban kuɗi, kuma ba wai ba shi da ne ba, dan soja ne, yana amsar albashi duk wata. Na samu lambarki a wani littafinki mai suna ‘Talauci Laifi ne’. A qarshe kin ba wasu shawara, kuma ki ka ce mai neman shawara zai iya tura saƙo ta wa’innan numbers. Shi ne ni ma na turo. Aunty Allah Ya qara basira da hazaƙa, littafin ya yi daɗi sosai. Na gode. ki huta lafiya. 

AMSA:

Zan soma amsa wannan tambaya da tambaya, don fahimtar da mai tambaya yadda za a yi saurin fahimta, shin don me ake soyayya tsakanin mace da namiji? Idan saurayi ya nemi budurwa da sunan soyayya ma’ana nawa hakan yake da su?

Amsa ta farko, ga sananniyar ma’ana, jinsin biyu, wato mace da namiji suka ƙaunace juna, to tabbas muradin su su mallaki juna, ko dai ta kyakkyawar hanya ko mummuna. Amsa ta biyu kuwa, ma’ana biyu ce, wanda dukkansu suna nuni da sha’awa, ma’ana ta farko don niyyar aure, ta biyu kuwa, don samun biyan buƙata, inma ta jima’i ko shirita.

Idan an fahimci shimfiɗar da muka yi, za a fahimci cewa, duk namijin da zai kusanto ko da sunan soyayya, to fa shi ne zai fara yi ma ki zancen aure, koda kuwa bai shirya ba, zai gabatar da maganar a ƙoƙarin bayyana muradin sa. Akasin haka kuwa za a iya fassara shi da yaudara.

Don haka ‘yar’uwa mai tambaya, kafin a kai ga zancen ke ba ki iya yi wa saurayin naki zancen ya turo, ki tambaye kanki, ko yana maki zancen auren, idan yana yi zan iya cewa ta maganar da yake yi ne za ki fito da zancen da iyayen naki ke faɗa na ya turo, wanda a nawa gani shi karan kansa ya ci ya riga ki furta wannan maganar idan da gaske yake.

Idan har yana yin zancen auren ke ce dai ba ki faɗa masa ba, ko don saboda kunya, to za ki iya amfani da zamani ki sanar da shi, kamar ta tura saƙo da sauransu. Idan kuwa bai taɓa yin magana ba ne, to kuwa da alamar tambaya, domin idan babu zancen aure, sai wane zance?

In kuwa zance na na kan hanya, zan iya cewa tun wuri ki san inda dare ya yi maki, tun kan wankin hula ya kai ki dare. Ki mayar da hankalin ki kan waɗanda ke neman ki da aure. Yadda za ki tabbatar kuwa, ki yi masa zancen auren ta kowacce hanya ta fi maki sauƙi. In har ya ƙi yi maki magana ƙwararra, to ki dawo rakiyyar lamarin shi, don inda ki ka dosa ba nan ya nufa ba. In ko zancen ba haka ba ne za ki gane daga irin abinda zai ce maki.

Sai zance na biyu, wato ‘yan dabaru da ki ka nema da zai sakar ma ki bakin aljihunsa, wannan dai kam ya wuce nawa sanin, sai dai abinda nake so in lurar da ke, akwai illa a saka rai ga abinda saurayi yake da shi, saboda sheɗan kan yi amfani da wannan ya ingiza ka ga ɓarna idan an yi dace da shawarakin saurayi.

Abu na biyu, ita kyauta da ki ke gani hali ce, kamar yadda za ki ga mai yawan surutu, da shuru-shuru, haka mai kyauta da kuma wanda hannunsa yake rufe. Idan saurayin ki ba ya maki alheri, yakan yiwu halinsa kenan, don haka ko da ‘yan dabarun ba za ki iya yagar wani abin kirki daga gare shi ba, ga kuma nisanta kanki da za ki yi da shi don kin nuna kina sha’awar abin hannunsa.

Ko kuma ya kasance yana gwada ki ne, ya ga ko kina son sa tsakani da Allah ko kuwa abin hannunsa ki ke so. Idan wannan ne, zan iya cewa abu ne mai sauƙi, saboda zai daina yayin da ya tabbatar kina son sa tsakani da Allah. 

Abu na ƙarshe zaɓin Allah shi ne zaɓi, don haka ki ba wa Allah zaɓi ta hanyar yin istihara da ta fito daga manzon rahma, ingantacciya da ba wata bayan ta. Idan ba ki san da ita ba, za ki iya ƙara nema na don sanar da ke. Ki bar wa Allah zaɓi, idan ba saurayin naki ne alheri ba, Allah Ya fitar da shi daga ranki, Ya karkatar da ke ga inda yake alkhairi. 

Allah Ya zaɓa maki mafi alheri.