Ta’aziyya: Ina fatan za a yi wa Hanifa adalci, inji Aisha Buhari

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Mai ɗakin shugaban Nijeriya, Aisha Buhari ta ziyarci Kano domin ta’aziyya ga iyalan Sheik Ahmad Bamba da kuma Hanifa Abubakar, yarinyar nan ‘yar shekara biyar da ake zargin mai makarantarsu ya kashe ta.

A jawabin da ta gabatar a gidan gwamnatin jihar Kano ranar Laraba, Aisha Buhari ta ce ta je jihar ne a ziyarar ta kashin-kanta domin jajanta wa gwamnan Kano da matarsa, da Sarkin Kano da kuma al’ummar jihar a kan rasuwar Sheikh Ahmad Muhammad Ibrahim Bamba da kuma Hanifa Abubakar.

Game da kisan da aka yi wa Hanifa, matar shugaban ƙasar ta ce tana fata tare kuma da addu’ar za a yi wa yarinyar adalci.

Ta ce: ‘’A matsayina na uwa ina da ‘ya’ya da jikoki waɗanda tuni suna makarantar firamare. Sun amince da malamansu sosai haka mu ma kuma.

“Saboda haka a yanayin da za a ce ‘ya’yanmu ba su tsira ba a makarantunsu, to lalle hakan na nuna ba shakka al’umma ta zama wani abu daban. Ina ganin ya kamata a yi hukuncin domin kwantar da hankali a Nijeriya.’’

Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya ba wa Aisha Buhari tabbacin cewa lalle za a tabbatar an yi adalci a kan kisan na Hanifa, wadda ya ce, ‘’Hanifa ‘yarmu ce kuma ‘yar ‘yan Nijeriya ce.’’

Mai ɗakin shugaban Nijeriyar ta kai ziyarar ta’aziyya gidan su Hanifa, inda ta yi wa iyayen yarinyar, wadda kisanta ya ɗauki hankali a Nijeriya, ta’aziyya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *