Tarbiyyar matasa: Duniya ina za ki da mu?

Daga SADIYA GARBA YAKASAI

Ga mu yau ma cikin filinmu mai albarka tare da ni Sadiya Garba Yakasai. Za mu duba matsalarmu ta gaba kan yara matasa ‘yan bana-bakwai da suka cusa kansu cikin rayuwa mara kyau. Samari yanzu sun lalace da abubuwan assha kala-kala, ba sa tsoro, babu imani cikin zuciyarsu balle su tuna da haƙƙin iyaye da suke ɗauka kullum. Mutane na tsinewa iyayen yara masu shiga haƙƙin mutane. Abun yanzu kowa tsoro yake ba shi yadda ake fito da yara ƙanana da ba su gaza shekara sha biyar ba zuwa ashirin da ɗoriya, su ne suke baje taɓargazar rashin imani da rashin kunya.

Wai iyaye ina za mu sa rayuwa ne? Ɗan da ka haifa yau a nuna maka shi ne uwa da uba, don ba ya gudun abun kunya, ba ya tsoron me zai ɗebo, kawai idanunsu a rufe su na aikata manyan laifukan da za a zata ƙato ne zai iya. Yanzu yaro ɗan shekara goma sha biyu sai ya yi abun da za ki shekara ba ki fita daga cikin tunaninsa da mamaki ba.

Yanzu waɗannan yara su ne masu tare hanya su ƙwace waya sun ma daina ta kuɗi kawai su waya ko mota. Waɗannan abubuwa su ne yanzu mutum idan ya yi wasa, ko ya yi jayayya ga waɗannan yara marasa kunya da imani, za su raba ka da Duniya gabaɗaya.

Mutane sun gaza riƙe waya a fili duk uzirinka, ba za ka amsa waya a tituna ba, yanzu za a karɓe. idan ka yi gardama su kashe ka ko ka yi jinyar da za a fasa kukan mutuwarka. Kuma hukuma na ji, na gani an kasa shawo kan wannan matsala, duk da ana ɗan kokartawa amma babu tsaro fa. Idan sun rasa waya su yanke ka, idan ka ba su in kana da rabon shaidarwa, ka yi sa’a su bar ka da ranka.

Ƙwacen waya yanzu ƙara ta’azzara yake daɗa yi cikin ƙasar nan. Yara sun shafa wa idonsu toka sun dage sai sun yi kuɗi ta kowacce hanya.

Idan ma ka ce ba za ka fita da waya ba, to ba ka tsira ba. Mota, babur duk suna cikin sammatsin rayuwa. Kuɗi a ATM ba su tsira ba, ya ilahil alamina ina za mu dosa? Iyaye anya ba mu yi sakaci ba kuwa?

Daidaita sahu shi ma da muke ganin sauƙi ne agurinmu, shi ma ya kusa daina shigowa. Sau da yawa masu abun sana’ar mashin ɗin ne ake haɗa baki da su ana wa fasinjoji ƙwace ko a sace mutum shikenan, sai dai a ji mugun labari. Ya Ilahil alamina me ya yi zafi?

Na fi ganin laifin gwamnati domin ita ta haifar da wasu matsalolin na rayuwar matasa. Sun gama makaranta, sun fita neman aikin da za su rufa wa kansu asiri da iyayensu su ci moriyar wannan ilimin, sun gaza samun aikin. Ga duniya ta canja mai hakan shi ma nema yake don me kuwa zuciya ba za ta gaya musu ƙarya ba, wallahi yanayi na rayuwa ya jefa matasa da yawa cikin halin ƙaƙa nika yi. Da za a ja su a jiki, gwamnati ta sama musu abun yi, wallahi da lafiya za a zauna. Wannan shi ke haddasa wa matasa mutuwar zuciya, shi yake sa su faɗawa cikin wata rayuwa.

Wani ma iyayen da za su tallafa masa ba shi da su. Yaro ya tashi babu ko sisin da zai karya. Ko ya yi buƙatunsa ya ga babu, ya je gurin iyaye su ba shi, su ma babu. Don Allah yaya zuciyar wannan yaro za ta yi? Daga nan fa zai fara jin rashin imani ya fara rutsa masa zuciya ya afka sana’ar da za ta jawo masa gurɓacewar rayuwa. Wannan har da laifin gwamnati. Da za a sama wa matasa abun yi, wallahi wani abun ba zai faru ba. To ita gwamnatin ma ina ta san ana yi kanta kawai da su kansu suka sani ba ruwan su da rayuwar yaran wasu, sun manta nauyin al’umma da suka ɗauka, za su cika wa kowa burinsu.

Duk abubuwan da suke faruwa abu biyu ne, sakacin iyaye na rashin bincikar yaransu me suke yi. Wa suke mu’amala da su? Ina suke zuwa? Ta yaya suke rayuwa? Uwa ta ga ɗa da sabon kaya ya sa, ya kuma riƙe waya babba a hannunsa. Amma ba za ta ce masa wane zo ina ka samu waɗannan abubuwa ba. Wata uwar ma daɗi za ta ji ɗanta ya samu cigaba, ya fi sauran yara. Ba bincike ba komai, haka za a sa masa ido yana ta faman fantamawa. Shi ma uba bai sa ido ya ga takun rayuwar da ɗansa ya sake ba, shi kawai idan ba za a tambaye shi komai ba, shikenan. 

Ko uwar ma ta faɗa masa halin da ɗan nasa ke ciki, amma tsabagen rashin tunani sai ya yi biris da ita. Sai komai ya lalace ya ce an cuce shi ba a sanar da shi ba. Shi ya sa wani sa’in laifin ya fi ƙarfi a iyaye. Akwai iyayen da sam ba sa son a gaya musu gaskiya sai su ce ana musu baƙin ciki an tsani yaransu don an ga Allah ya ɗaukaka shi za a cinye musu ɗa da baki. Sai komai ya kancame kuma, su fara nadama.

Abu na biyu shine, gwamnati dole ta gyara ta sa ido sosai a kan tsaro ta kuma sama wa yara matasa abun yi ko da tashin wasu kamfani ne dai da yaro zai je ya yi aiki ya samu na buƙata da za a samu sauƙin wannan ibtila’i da yara suka shiga .

Tunani ya fara kufce wa mutane. Kana ta abinci kuma ba ka da shi, ba ka kuma da mai ba ka. Komai ya ƙare a kan talakawan.

Don Allah iyaye mu farka,  mu sa wa yaranmu ido. yanzu duk inda ka duba ko ka juya, zancen ɗaya ne,  yadda yara matasa suka lalace da mugwayen ayyuka: su ne sata, su ne kashe mutum su ɗauke masa waya, su ne satar mota, su ne shaye-shaye, su ne garkuwa da mutane. Ya Ilahil alamina, ina za mu sa kanmu ne? Amma idan uwa ta sanya ido, dole fa tun baya ji, watarana zai ji. 

Wasu kuma iyayen ne ma da kansu suke sa yaran su satar. Eh mana, uwa za ta bar yaro ba aikin yi, kuma ba ta kawo komai ta ba  shi ba, ya zama lusari. Tun ɗa yana hakuri yana shiru, watarana zai ba ta amsa dai-dai da kalamanta, shi ne zai fara mugun sana’ar da za ta zo tana kuka babu halin gyarawa. Don haka, mu kiyaye harshenmu a kan yara. Wallahi a yi ƙoƙarin nuna musu rayuwa da hikima ba da faɗa ba, don Allah mu kiyaye. Abunda babba ya hango fa, yaro ko rimi zai hau ba zai ga komai ba, sai wahala.

Rashin bawa yara mahimmancin ilimi shi ma ya taka wata rawa akan gurɓacewar yaran, don tun yaro yana cewa ba zai je makaranta ba, iyaye ba sa tilasta musu zuwan. Ko in sun je ba sa bincike ayyukansu na makaranta shi ma ya taka rawa wajen dakushe musu karatu.  Don ilimin daga yaro ya fara gudun makaranta, shikenan iliminsa ya lalace. Barin yara sakakkai babu kwaɓa, komai suka yi dai-dai ne. Yaro idan ya dawo makaranta ba za a duba me ya yi a makarantar ba. 

Ya yi wanka,  ya fice yawo. Ba za a gan shi ba tsahon lokaci ba tare da an sa masa ido ba. Uwa ba za ta tambaye shi ina ya je ba. Kawai sai shi kuma ya cigaba da aikata yadda ya so don ya san bai da damuwa da iyayensa. Ba faɗa za a masa ba. Daga nan sai shiga rukunin ɓata-garin yara. Yau suna can, gobe suna can. Dare ya yi yaro ƙarami ya ci wanka ya tafi kulob da yara, ba za su dawo ba sai tsakar dare.

Wani ma uban bai damu da ya binciko yaron yana gida ba ko a’a ba, shi ma kawai kwanciyarsa zai yi. Idan uwa mai ƙwauron baki ce, ba za ta faɗa wa uban fa cewa ga halin da da ɗansu ya faɗa ba. Daga nan sai rashin kwana a gida. Shi ne cikin unguwa, da wajen masu shaye-shaye da sauransu. Duk da wasu iyayen sun sani tsabar son yara ne ya sa ba za su tsawatar musu ba, kar ɗa ya yi fushi.

Wannan ko ba rayuwa ba ce. idan har uwa da uba za su zuba ido yaro ya yi yarda ya so, to gaba akwai aiki wallahi.
Wani a waje za a koya masa shaye-shaye idan ya yi nisa ba tare da iyaye sun lura ba, shikenan sai kuma ɗauke-ɗauke, daga nan sai ƙwace. Yanzu ga su nan sun cika gari a wannan sana’a. Wasu ma daga ƙauyuka suke zuwa, wasu daga wasu garuruwan suke zuwa, kawai su yi sata su koma.

Ta yaya za a yi uwa ta ga ɗanta da babbar waya da suttura ta gani, ta faɗa ta kasa cewa komai, bayan ta san ba ita ta ba shi ba, ba ubansa ne ba? Amma sai ta yi shiru kawai kar ɗanta ya yi fushi. Wallahi da mutane za su ringa zuwa kotu ko ofishin ‘Yansanda, da sun ga yadda ake kai yara ƙanana, duk kuma a kan satar waya ne ko mota. Wasu kuma sun kashe masu wayar . Allah ya kamata gwamnati ta sa tsaro a tituna don yanzu a tituna ake wannan ta’asar.

A nan za mu tsaya sai sati mai zuwa. Allah ya sa muna raye, Allah ya ba mu ikon kyautata wa iyalinmu. Ma’assalam.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *