Dokar mai: Yadda cacar baki ta kaure a majalisa kan Bauchi, Legas da Ogun

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Yayin zaman Majalisar Dattawa na jiya Alhamis, wata ‘yar hayaniya ta kaure yayin da aka gabatar da dokar da za ta saka wasu jihohi uku a jerin masu fitar da man fetur a Nijeriya, a cikin garambawul ɗin da ake yi wa Hukumar NDDC.

Sanata Adeola daga jihar Legas, shi ne ya gabatar da ƙudirin wanda ya ƙunshi saka jihohin Bauchi, Legas da Ogun cikin jerin jihohi masu samar da albarkatun man fetur ɗin, sai dai lamarin bai wa sanatocin da suka fito daga yankin Neja Delta daɗi ba, inda suka yi fatali da ƙudirin.

Har wa yau, garambawul ɗin zai ƙunshi saka waɗancan jihohi uku da kuma wasu da suka fara samar da albarkatun man fetur a Nijeriya.

Jihohi 9 da ke cikin hukumar NDDC sun haɗa da, Kuros Riba, Edo, Delta, Abiya, Imo, Bayelsa, Ribas, Akwa-Ibom da kuma Ondo. 

A zaman majalisar, ƙudirin ya samu tsallake karatu na biyu, wanda Sanata Solomon Olamilekan Adeola na jam’iyyar APC daga Lagas ya gabatar da shi. 

Adeola ya ce tuni jihohin Bauchi, Legas da Ogun suka shiga jerin masu samar da ɗanyen man fetur, bayan gano albarkatun mai a Alaaleri, Badagry da Ipokia. 

A cewar Sanatan “Bisa adalci, jihohin sun cancanci samun kashi 13 da ake ware wa jihohin da ke samar da ɗanyen mai kamar yadda sashi na 162 cikin baka na 2 na kundin mulki ya tanadar.”

“Maigirma Shugaban Majalisa, na gabatar da wannan ƙuduri ne domin waɗannan jihohi su shiga jerin masu albarkatun mai da ma wasu da za a iya samu nan gaba.” 

A nasu martanin, sanatocin yankin Neja Delta, sun yi watsi da ƙudirin na ƙoƙarin saka jihohin Bauchi, Legas da Ogu cikin NDDC. Sanata George Sekibo (PDP daga Jihar Ribas) da Sanata Matthew Urhoghide (PDP daga Jihar Edo) da Sanata Ovie Omo-Agege (APC daga Jihar Delta), sun ce an ƙirƙiri NDDC ne domin magance gurɓatar muhalli a yankin. 

Urhoghide ya ce jihohin da ke wajen Neja Delta na da damar samun tagomashin kashi 13 da ake warewa, amma ya jaddada cewa saka su a NDDC ya saɓa wa doka. 

Sanatocin sun roƙi Adeola ya canza tunani, ya nemi a samar da hukumar da za ta duba yanayin a yankin Kudu maso Yamma, maimakon neman saka Legas da wasu a cikin NDDC. 

A ɗaya hannun kuma, sanatocin shiyyar Arewa, sun nuna goyon bayansu ga ƙudirin amma sun nuna cewa jihohin da ke wajen yankin Neja Delta bai kamata su shiga NDDC ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *