Yaƙi da ta’addanci: Sojojin sama sun yi ruwan bama-bamai kan dandazon mayaƙan ISWAP

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

An samu nasarar kawar da ’yan ta’adda da dama yayin da jirgin yaƙin rundunar sojin sama (NAF) ya saukar da ruwan bama-bamai kan taron dandazon mayaƙan ISWAP.

Rahotanni sun nuna cewa, jirgin yaƙin ya hallaka wasu tare da jikkata da dama a Sabon Tumbun da Jibularam da ke ƙaramar hukumar Marte duk a jihar Borno.

’Yan ta’addan sun gamu da ajalinsu ne ranar Jumu’a, daga harin bama-baman jirgin sojoji, yayin da suke tsaka da gudanar da gagarumin taro tare da sabon shugabansu, Sani Shuwaram.

Ƙarin bayani na nan tafe…