Dalilina na banke ɗan jaridar Vanguard da mota – Wanda ake zargi

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Wani mai suna Clement Itoro, ɗan shekara 29 da ’yan sanda suka kama bisa zargin kashe &an jaridar Vanguard, Tordue Salem, ya bayyana dalilinsa na aikata laifin.

A cewar Itoro, ya kashe marigayin ne ta hanyar banke shi da motarsa sannan ya gudu saboda ya yi zaton shi ɓarawo ne.

Itoro, wanda ya kasance direban motar kabu-kabu ya yi bayanin cewa ya banke marigayin ne a yankin Mabushi da ke babbar birnin tarayya, Abuja.

Ya bayyana hakan ne a lokacin da kakakin ’yan sandan ƙasar, Frank Mba ya gurfanar da shi a hedikwatar rundunar IRT, Abuja, a ranar Juma’a, 12 ga watan Nuwamba.

Da yake zantawa da manema labarai yayin gurfanar da shi, Itoro ya ce, lallai ya banke wani mai tafiya a hanya da bai sani ba da misalin ƙarfe 10 na daren ranar 13 ga watan Oktoba.

Sai dai, ya ce, bai tsaya ya kula da ko wane shi ba saboda yana tsoron kada ’yan fashi su far masa, sanin cewa yankin Mabushi wuri ne mai haɗari inda ya kasance sanannen matattarar ’yan fashi ne, don haka ya tsorata.

Ya ce, “na yi zaton mutumin da na banke &an fashi ne sai washegari da na ga wani fasasshiyar waya a gilashin gaban motana, amm wayar bata aiki don haka sai na jefar da ita. Wajen da na bige wannan mutumin, kowa ya san cewa wajen ’yan ta’adda ne.”

Da yake gurfanar da wanda ake zargin, Mba ya fada wa manema labarai cewa an kama Clement ne sakamakon wani bincike da sashin ƙwararru na rundunar ta aiwatar.

Ya ce, Clement wanda ke tuƙa wata motar Camry ƙirar 2004 da lamba BWR 243 BK ya tona cewa shi ya banke Salem da misalin ƙarfe 10:00 na daren ranar 13 ga watan Oktoba, 2021, a yankin Mabushi da ke Abuja amma sai ya gudu.

Gani na ƙarshe da aka yi wa Salem wanda ya kasance ɗan asalin jihar Benue ne, ya kasance a ranar 13 ga watan Oktoba, 2021, lamarin da ya haddasa cece-kuce a ƙasar.