Ƙarya ta ƙare kan batun Mambila!

*Babu sauran tarnaƙi tunda Kamfanin Sunrise ya janye ƙararsa – Malami
*Gwamnati na iya yin sulhu da Kanu da Igboho, inji Ministan Shari’ar

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Ministan shari’a kuma Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya), Abubakar Malami, ya bayyana cewa, kamfanin samar da wutar lantarki na ‘Sunrise Power Transmission Company of Nigeria Ltd’ (SPTCL) ya watsar da shari’ar da ya ke yi wa Gwamnatin Nijeriya, lamarin da ya kai ga kawo jinkiri ga aikin samar da wutar lantarki na Mambilla, yana mai cewa, a yanzu hakan na nuni kenan da babu sauran tarnaƙi wajen cigaba da aikin samar da wutar lantarki da ake yi a yankin na Manbila.

Bugu da ƙari, Ministan Shari’ar ya kuma bayar da haske kan yiwuwar yin sulhu da masu rajin ɗaiɗaitawa ko tsintsinka Nijeriya ɗin, Nnamdi Kanu da Sunday Adeyemi Igbpho.

Da ya ke amsa tambaya kan tsarin sasantawa da aka daɗe a lokacin da yake amsa tambayoyi daga ’yan jarida, Malami ya ce, faɗan da ake yi na shari’a ya haifar da cikas wanda ya hana saka hannun jari a aikin Manbila daga Ƙasar Chana.

A watan Agusta ne gwamnatin tarayya ta umurci Hukumar Kula da Zuba Hannun Jari ta Nijeriya (NSIA) da ta tuba kuma ta biya dala miliyan 200 ga kamfanin.

“Sunrise ta janye ƙarar da ta ke yi game da shari’ar da ta saɓawa muradun gwamnatin tarayya wasu kuɗaɗe da ke bin yankin kusan dala biliyan ɗaya,” inji shi.

“Saboda haka, kasancewar shi ne kawai cikas ga aikin Mambilla, wanda ya kasance shari’ar da ake jira wanda ya haifar da cikas wanda ya hana ma su saka hannun jari a Mambilla aiki, tare da dakatar da shari’ar yanke hukunci ta Sunrise.”

Ministan ya ce, dakatar da shari’ar a birnin Paris na buƙatar a yi farin ciki sosai.

Sulhu da Kanu da Igboho:
Ministan Shari’a kuma babban lauyan Gwamnati Tarayya, Abubakar Malami, ya ce, Gwamnatin Nijeriya za ta iya la’akari da duk wata hanya wajen kawo ƙarshen rikicin da masu neman a varka ƙasar su ke neman jawowa.

Malami

Rikicin da shugaban masu fafutukar kafa ƙasar Biyafara (IPOB), Mista Nnamdi Kanu, da na fafutukar ƙasar Yarabawa, Mista Sunday Adeyemo (wanda aka fi sani da Igboho) ke yi, ya haifar da rikici da tashe-tashen hankula, musamman a yankin Kudu maso Yamma da kuma Kudu maso Gabas, wanda ya kai ga yin kiran a kawo ƙarshen irin waɗannan rikice-rikicen.

Da yake magana a wata tattaunawa da manema labarai a Abuja, Malami ya bayyana cewa, gwamnatin Nijeriya za ta iya neman mafitar siyasa a wajen kotu da irinsu Nnamdi Kanu da kuma Sunday Igboho.

Ya ƙara da cewa, “idan akwai wata hanyar za a duba yiwuwarta, za mu bincika don duba sahihancinsa, da kyakkyawar niyya da ke tattare da ita, da kuma fitar da abubuwa ma su yawa da suka shafi tattaunawa ko akasin haka.”

Ya ce, gwamnati na duba laifukan da aka aikata tun a matakin farko don haka ne Igboho da Kanu ke fuskantar shari’a. Kuma idan aka aikata wani laifi, gwamnati na da ɗaukar matakai na musamman wajen tabbatar da cewa mutanen da aka yi amfani da su ta wata hanya ko ta wata hanya an gurfanar da su a gaban kotu.”

Da aka tambaye shi dalilin da ya sa gwamnati ta kasa bayyana sunan wani Sanata da ta ce shi ne ke da alhakin gudanar da aikin Ighobo, Malami ya ce, gwamnati na kan haka kuma za a san cikakken bayani idan aka gurfanar da waɗanda ake zargin a gaban kotu.