Tare Da AMINA YUSUF ALI
Barkanmu da sake haɗuwa a wani makon a shafinmu mai albarka na zamantakewa mai zuwa daga jaridarku mai farin jini, Blueprint Manhaja. A wannan mako muna tafe da dalilan ko na ce tasirin da ya sa ya kamata a fara nema kafin a kai ga aure.
Nema dai a aure shi ne zaman da saurayi da budurwa ko bazawara suke yi na soyayya kafin a kai ga aure. Inda saurayi/magidanci zai ta ziyartar budurwa/bazawar (zance), da yi mata waya a kai-a kai har su fahimci juna, sun amince da juna, sannan daga bisani ya turo iyayensa a zo a yi maganar aure.
A wannan zuwa zance da namiji ke yi gun budurwa ko bazawara yana yi mata kyaututtukan da za su zama kamar toshiyar baki a kan ta zave shi fiye da sauran samarinta. Haka har ya kai ga nasara ko akasinta. Kuma wannan kyautar tana nuna wa yarinya da iyayenta lallai wannna saurayin da gaske yake ba wai da wasa ya zo ba.
A zamanin da a al’adar Bahaushe, yawanci iyaye ne kan zava wa ‘ya’yansu mata da maza abokan rayuwa wato miji da mata. Kuma wani zubin za a bar su su yi ta zance har su fahimci juna sannan a yi aure. A zamanin da ma akwai wani abu da ake kira tsarince da ake yi.
Amma wannan tun zamanin kafin Bahaushe ya karɓi addinin islama ne. Haka wani auren haɗin ma ko ganin juna ba sa yi ake yin auren. Sai dai kuma a yanzu zamani ya canza. Yaran ne suke fara haɗuwa da juna har su fara tattaunawa kafin ma iyayen nasu su sani. Sai daga baya ma idan maganar ta yi ƙarfi suke shigo da iyayensu cikin maganar.
Duk da dai a da akan yi aure ba tare da zancen ko nema ba, amma shi ma neman yana da nasa irin tasirin a aure. Kuma ba wai rage dare za ka je gun ta ba, ta yi maka samartaka ka yi mata ‘yammatanci ba. Akwai tasiri sosai a neman aure. Ga wasu daga cikin muhimman alfanu na neman aure.
- Zuwa zance wajen budurwa/bazawara yana ƙara muku fahimtar juna, da gane halayyar juna, da kuma fahimtar abinda wani yake so da ƙi domin kiyayewa. A nan za ku fahimci ma waye wanda kuke son auren? Y yi miki? Sannan kuma auren zai ɗore idan an yi? Yaya yake ganin yadda yake girmamaki da iyayenki? Da dai sauransu.
Kai ma za ka duba tarbiyyarta, da iyayenta da gidansu bakiɗaya. Ta yi maka a matsayinta na macen da za ka yi rayuwa dindindin? Tana da tarbiyyar da za ta iya ba wa yaran da za ku haifa? Za ta girmama iyayenka? Idan aure za ka ƙara, za ta iya kawo maka zaman lafiya da sauran iyalanka ko rusa maka gida za ta yi? Da dai irin sauran abubuwa da za ka fahimta. - Zuwa zance yana ƙara wa masu son yin aure a tsakaninsu shaƙuwa, wanda shaƙuwa wani abu ne mai muhimmanci a aure. Don tana kawo zaman lafiya sosai a aure.
- Ba wa yarinya damar yin zance da samari amma ba barkatai ba yana ba wa samari da ‘yammata damar yin mu’amala da wasu masoyan domin su ɗan ƙara fahimtar rayuwar aure da mu’malarsa. Domin kowanne mutum da halinsa. Haka zai ba su damar ganewa da tantace wanne irin abokin rayuwa ya kamata su zaɓa.
- Zai sa ka saba da iyaye da danginta dai-dai gwargwado son samun mu’amala mai kyau bayan kun yi aure.
- A yayin neman aure ne za ku fuskanci yadda za ku dinga samar da maslaha idan wata matsala ta faru a tsakaninku.
- Fahimtar wasu baqin ɗabi’u da ɗayanku yake da shi ko naqasu ba sai har an kai ga aure ba sannan a gano abin ya zama ba daɗi. Amma ko ma meye idan aka gano shi wataqila a saba da shi kafin aure. Idan ma ba a saba ɗin ba, za a iya auren a haka amma dai an sani ɗin ya fi a ce ba a sani ba.
Duba da waɗannan dalilai, kenan nema a aure yana da matuqar muhimmanci. Don haka ya kamata a dinga haɗuwa da juna da yin waya ana tattaunawa musamman a gidan su matar don gudun keta Shari’a.
Sannan kuma bai kamata a shigo da wata harka ta alfasha ko keta dokokin Allah ba. Shi ya sa idan ba ya zama dole ba, kada mace da namiji da suke da niyyar auren juna su keve su kaɗai, don shaiɗan yana iya ribatarsu.
Hadisi ya zo da Manzo Sallallahu alaihi Wasallama yake cewa, mace da namiji ba za su keve ba, har sai shaiɗan ya zama na ukunsu. Don haka, kada ki yarda ki keve da mai neman aurenki. Idan kika bari kuka aikata alfasha kun sava wa Allah kuma da wuya ya ƙara amincewa ya aure ki. Zai dinga tantama a tarbiyyarki. Idan ma ya aure ki ɗin, ba lallai auren ya yi ƙarko ba don kun riga kun kwashe albarkar auren.
Kuma yana da kyau ku ba wa junanku isasshen lokacin da za ku iya fahimtar juna. Domin fa auren juna kuke so ku yi. Kuma shi aure ana yin sa har muddin rayuwa. To idan ba ku fahimci juna ba haka za ku yi ta fama kuma ba san idan an yi auren yaushe zai ƙare ba. Ko idan ka yi.
Don haka a yi nema kafin aure kuma a kula sosai. Sai wani makon idan rai ya kai. Ina godiya ga makaranta. Allah ya bar zumunci masu kirana da fatan alkhairi, ina godiya matuƙa.