Buhari ne silar shiga halin da ‘yan Nijeriya suka shiga a yau

Daga NAFI’U SALISU

Al’amarin shugabancin ƙasarmu Nijeriya yana cike da abin al’ajabi da mamaki, game da yadda abubuwa su ke gudana, wanda hakan ya sa a kodayaushe ‘yan ƙasar ke buƙatar sauyi. Sai dai halin da ƙasar ke ciki a yanzu, ya zamo sanadin da ya sa ‘yan Nijeriya da dama ɗebe tsammani a kan samun salamar da suka daɗe suna fatan samu.

Kafin zuwan Buhari da Gwamnatinsa, talakawan Nijeriya suna rayuwa a cikin salama, duk da cewa akwai gurvatattun abubuwa irin su cin hanci da rashawa, halasta kuɗin haram da ayyukan ta’addanci kamar Boko haram.

A cikin kashi ɗari, akwai kashi sittin da biyar (65%) na rayuwar sauqi a Nijeriya, kashi 35% na matsalolin Nijeriya, Boko Haram na da kashi 25% yayin da sauran matsaloli suke da 10%, kashi goma cikin ɗari.

Duk da cewa al’ummar Nijeriya sun yi fatan samun sauyi a Gwamnatin tsohon shugaban ƙasa Buhari, wanda dalilin hakan ne ma ya sa aka zave shi saboda kyakkyawan zaton da al’ummar Nijeriya (musamman talakawa) suka yi masa, amma maimakon kyakkyawan fata da zaton da ‘yan Nijeriya suka yi masa ya tabbata, sai ma ƙara taɓarɓarewar da al’amura suka yi.

Da dama daga cikin al’ummar Nijeriya sun ta zuba idon ganin al’amurran ƙuncin rayuwa sun yi sauƙi a ƙasa a wancan lokacin, to amma sai rayuwar ta ƙara tsananta, ‘yan ƙasa suka ƙara shiga cikin mawuyacin halin ƙa-ƙa-ni-ka-yi.

Baya ga tashin gwauron zabi da kayan masurufi suka yi, akwai ƙaruwar ayyukan ta’addanci da suka ƙara ruruwa tamkar wutar daji. Man fetur da Diesel (Gas) suka ƙara kuɗi, abin da ya haifar da hauhawar farashin kayan abincin. Hakan ya sa da dama suka haqura da amfani da abin girki (Gas cooker) wajen yin girki suka koma amfani da gawayi.

Gwamnatin tsohon shugaban ƙasa Buhari ta ƙara jefa al’ummar Nijeriya cikin ƙunci sakamakon ƙarin haraji da kuɗin man fetur, da ƙirƙirar asusun ajiyar Banki na bai-ɗaya wato (single account), rufe iyakokin ƙasa (Borders), canjin kuɗi da aka kira da (cash policy), da sauran abubuwa da dama.

Abu na farko da ya fara zamowa babbar matsala a salon mulkin tsohon shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari, bai wuce rashin iya tafiyar da mulki ba. Hakazalika, salon mulkin tsohon shugaban ƙasa Buhari, salo ne da za a iya kira da ‘Salo mara kan gado’, domin ko a zaɓen abokan ayyuka da za su taimaka masa don ciyar da ƙasa gaba, bai zaɓi jajirtattu masu kishin ƙasa ba.

Bayan haka, dukkan salo da tafiyar da jagoranci a gwamnatinsa, babu tausayawa wajen takura ‘yan ƙasa da tunanin halin da za su shiga. Misali idan mu ka kalli yadda tsohon shugaban ya rufe iyakokin ƙasa ba tare da an samar da abubuwan da za su hana ƙasar shiga halin ƙunci ba, ta fuskar rayuwar yau da kullum.

Batun ƙarin haraji da kuɗin wutar lantarki, da rufe iyakokin ƙasa, da canjin kuɗi da Gwamnatin Buhari ta yi, su ne ummul’aba’isin jefa ‘yan Nijeriya cikin mawuyacin halin da a yanzu ya same mu a Nijeriya.

Duk wasu dalilai da tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya kafa hujja da su a kan canza kuɗi, dalilai ne marasa tushe balle makama, domin yin canjin kuɗin bai zamo alkairi ga talakawan Nijeriya ba, sai ma jefa al’umma cikin masifa da hakan ya yi.

Duba da wannan hali da a yanzu ‘yan Nijeriya suke ciki, za a iya cewa kwata-kwata mulkin tsohon shugaban ƙasar Nijeriya Buhari bai amfanawa talakawa komai ba, sai baƙar wahala da koma-baya, domin hatta da tattalin arzikin ƙasar Buhari ya ɗai-ɗaita shi.

Babu wani abin da tsohuwar Gwamnatin Buhari ta tsinana face talauci da yunwa gami da taskun rayuwa da a yanzu ya zamo hantsi leqa gidan kowa. Ba maganar shinkafa ake yi ba da tuni ta riga da tafi ƙarfin talaka sai masara, wanda a yanzu masarar tafi shinkafar tsada, tunda a yanzu ta kai Naira dubu sittin (60,000), duk buhu ɗaya.

Babban abin takaici shi ne, idan muka kalli yanda canjin kuɗi ya sa mutanen karkara da na birni suka tafka asarori da dama, sai dai asarar ta fi shafar mutanen ƙauyuka. Domin a lokacin canjin kuɗi, haka suka riƙa fito da kayan masarufi suna sayarwa a kuɗi kaɗan, buhun masara har dubu 11,000 a ka riqa siya da sabbin kuɗi, idan tsohon kuɗi za a ba ka kuma dubu 18,000 ko ashirin. To tsaffin kuɗin kuma idan talaka ya karɓa bai san ina zai kai ba.

Haka wannan mummunan al’amari ya faru, daga baya kuma sai ga shi Gwamnatin Buharin ta bada sanarwar mutane su ci gaba da karɓar tsaffin kuɗin, su sabbin dama ba su wadata ba. Idan muka kalli iya wannan kaɗai, wanne ci gaba za mu ce Gwamnatin da ta shuɗe ta Buhari ta tsinanawa ‘yan ƙasa?

Tabbas! Tsohuwar gwamnatin Muhammadu Buhari tayi wa ƙasarmu illar da sai an daɗe kaɗin mu farfaɗo daga suman da muka yi a sanadin salon mulkin Buhari, domin hatta yara qanana da ba su gama mallakar hankulansu ba, sun ɗanɗani ɗaci da uƙubar mulkin Buhari mai cike da ragon azanci.

Nijeriya tana buqatar shugabanni ma su tausayi, waɗanda suka karanci menene tattalin arziki, ba wai shugabanni marasa kan-gado da mugunta da iya jagorancin al’umma irin tsohon shugaban ƙasa Buhari ba.

Da wannan nake ba wa ‘yan majalisunmu na wannan sabuwar gwamnatin shawara, ya kamata su zamo masu kishi a kanmu da ƙasarmu, domin Nijeriya ƙasa ce da Allah ya yi wa tarin albarka da arziki, idan har a ka sa kishi da tausayi, to ƙasarmu za ta dawo hayyacinta.
Nafi’u Salisu

Marubuci/manazarci ne mai sharhi a kan al’amuran yau da kullum. Ya rubuto daga jihar Kano.
Imel: [email protected]
[email protected]