Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
A ranar Litinin ne shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ƙara ƙaimi wajen mayar da Nijeriya sahun gaba wajen zuba jari a nahiyar Afirka ta hanyar tattaunawa da manyan ’yan kasuw masu zuba jari, Hakeem Belo-Osagie na Metis Capital da Bayo Ogunlesi na Global Infrastructure Partners & BlackRock.
Kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya ya bayar da rahoton cewa, babban taron, wanda aka gudanar a Legas, ya mayar da hankali ne kan buɗe manyan ayyukan zuba jari a fannin mai, iskar gas, da kayayyakin more rayuwa a Nijeriya, muhimman wuraren da gwamnatin ke kallo a matsayin gunshiƙan ci gaban tattalin arziki na dogon lokaci da ci gaban ƙasa.
An ba da cikakkun bayanai game da taron a kan tabbatacciyar hanyar sadarwar shugaban ƙasa, @officialABAT, inda ya jaddada gaggawar jawo babban canji a ɓangaren mai da iskar gas da manyan ayyukan more rayuwa.
“Mun amince da gaggawar buɗe manyan saka hannun jari a cikin mai da iskar gas da muhimman ababen more rayuwa don fitar da ci gaban Nijeriya na dogon lokaci,” inji Tinubu.
Shugaban ya tabbatar wa maziyartan sa cewa sauye-sauyen da gwamnatinsa ke aiwatarwa sun riga sun sake fasalin yanayin zuba jari, da buɗe hanyoyin samar da kuɗaɗe masu ɗorewa da kuma haɗin gwiwa a duniya.
“Sabunta tsarin gwamnatinmu na samar da yanayi mai kyau tare da bude sabbin iyakokin don samar da kuɗaɗe mai ɗorewa, ginshiƙin ci gaban duniya, da ayyukan kawo sauyi. Mun ƙuduri aniyar sanya Nijeriya ta zama cibiyar zuba jari a Afirka,” inji shi.
Dukansu Belo-Osagie da Ogunlesi suna mutunta sha’anin kuɗi na ƙasa da ƙasa. Belo-Osagie, shugaban kamfanin Metis Capital, ya daɗe yana jan hankalin masu zaman kansu da ke shigowa Afirka, yayin da Ogunlesi, wanda ya kafa Global Infrastructure Partners kuma mai gudanarwa na yanzu a BlackRock, yana kula da ayyukan duniya na biliyoyin daloli na makamashi da ababen more rayuwa.
Manazarta sun ce taron ya nuna yunƙurin gwamnatin Tinubu na ƙarfafa kwarin gwiwar masu zuba jari na ƙasa da ƙasa biyo bayan sauye-sauye masu tsauri da suka haɗa da kawar da tallafin man fetur da samar da sassaucin kuɗin musaya, da nufin daidaita tattalin arziki da kuma jawo jarin ƙasashen waje.
Gwamnatin ta yi fatan cewa haɗin gwiwa da manyan masu nauyi na duniya kamar Ogunlesi da Belo-Osagie ba kawai za su sake inganta muhimman ababen more rayuwa da haɓaka samar da mai ba har ma da ƙarfafa kwarin gwiwar masu saka hannun jari kan yuwuwar ci gaban Nijeriya na dogon lokaci.
