Otedola ya buƙaci Tinubu ya tona asirin masu badaƙalar tallafin mai

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Hamshaƙin attajirin nan na Nijeriya, Femi Otedola, ya buƙaci shugaban aasa Bola Ahmed Tinubu da ya bayyana cikakken rahoton kwamitin da Aigboje Aig-Imoukhuede ya jagoranta kan yadda ake badaƙala kan tsarin tallafin man fetur da aka yi a zamanin tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan.

Otedola, a cikin wata sanarwa da ya fitar a yammacin ranar Lahadin da ta gabata, ya nace cewa ‘yan Nijeriya sun cancanci sanin gaskiya game da waɗanda suka wawure baitul malin ƙasar ƙarƙashin shirin Asusun Tallafawa Man Fetur (PSF), wanda ya karkatar da biliyoyin daloli a ƙasar.

A cikin sanarwar, Femi Otedola ya bayyana cewa hankalinsa ya kai ga wani batu da Umar Sani ke yada wa, wanda ke danganta kamfaninsa da cin gajiyar tallafin mai fetur.

Ya bayyana cewa, “Yana ƙoƙarin karkatar da gaskiya da ƙoƙarin bata min suna da hanyar dangantaka ni badaƙalar tallafin man fetur a ƙasar nan.

“Duk waɗannan kalaman ƙarya ne, marasa tushe, kuma ƙoƙari ne na yaudarar jama’a da sauya abin da ya faru.”

Hamshaƙin ɗan kasuwar ya nanata cewa kamfaninsa na ‘Zenon Petroleaum and Gas’ bai taba cin moriyar tallafin man fetur daga gwamnatin Nijeriya ba.

A kalamansa, “Zenon Petroleum and Gas Limited kamfani ne da ya taɓa shigo da dizal kaɗai, sama da 90% a kasuwa, kuma bai taɓa yin kasuwancin man fetur ba. Saboda haka ba zai taɓa yin iƙirarin tallafi a ƙarƙashin tsarin talafin man fetur ba. An riga an cire Dizal daga tsarin tallafi.”

Otedola ya ƙara bayyana cewa shi ne ya tona asirin cuwa-cuwar tallafin man fetur a lokacin gwamnatin tsohon Shugaba Goodluck Jonathan, kuma akwai rahoto da ya tabbatar da haka.

Ya ce, “Ni ɗan kwamitin tattalin arzikin Shugaba Goodluck Jonathan. Ni ne na fara sanar da Shugaban ƙasa game da babbar badaƙalar da ake yi a tsarin tallafin man fetur. Da ya kira tsohuwar Ministar Man Fetur, ta musanta.

“Amma da na ga ba zan bari abin ya ci gaba ba, na kira Sanata Bukola Saraki na shaida masa. Shi kuma ya kai maganar gaban Majalisar Dattawa, daga nan majalisar wakilai ta fara bincike. Idan ni mai hannu ne a damfara, shin ni zan kai ƙarar kaina?” 

A kan batun tsohon ɗan majalisa Farouk Lawan, Otedola ya ce, “Da aka san ni ne mai tona asiri, sai masu hannu a damfarar suka fara mayar da martani ta hanyar amfani da kwamitin majalisa da Hon. Farouk Lawan ke jagoranta, suna ƙoƙarin tuhumata ba bisa ƙa’ida ba.”

Ya ce, sun shi da hukumar DSS ne su ka shirya wa ɗan majalisa Farouk Lawan gadar zare ta hanyar mika masa kuɗin cin hanci da aka riga aka yi wa alama.

Otedola ya yi kira ga Shugaba Tinubu da ya bayyana cikakken rahoton binciken Aig-Imoukhuede domin ‘yan Nijeriya su san ainihin abin da ya wakana.

By ukarofi