An yi kira ga Gwamna Raɗɗa ya gyara hanyar Joɓawa a ƙaramar hukumar Mani

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Al’ummar yankin Joɓawa da ke ƙaramar hukumar Mani, na yin kira ga Gwamnan Jihar Katsina Malam Dikko Umaru Raɗɗa da ya gyara masu hanyar su da ta ratsa garuruwa fiye da 20.

Da yake magana da manema labarai a madadin alummar garin malam Lawan Liman Joɓawa ya bayyana cewa yanzu haka ko mota bata shiga garin su, sai dai ayi amfani da mashina ko jakai ko kuma amalanke.

Lawan Liman ya ce ko marar lafiya ke gare su, saboda rashin kyan hanya, kafin akai shi Asibiti ya rasa ranshi.

Hanyar dai an yi ta ne tun lokacin mulkin shugabar ƙaramar hukumar Hajiya Yaha Mani, wadda itace a wancan lokacin tayi masu hanyar birji, amma yanzu hanyar bata shigowa garin na Joɓawa da garuruwan da ke gaba da garin.

Ya bayyana cewa ko a lokacin yaƙin neman zaɓe, sai da Gwamnan Jihar Katsina Malam Dikko Umaru Raɗɗa ya yi masu alƙawarin yin hanyar, amma har yanzu shiru ka ke ji.

Liman Lawal ya ƙara da cewa, garin Joɓawa na cikin tashin hankali musamman yadda hanya ɗaya da ke zuwa garin, yanzu mota ba ta iya isa cikin ta.

Ya bayyana cewa, ko rasuwa aka yi, sai dai al’ummar garin su je bakin rafi su ɗauko gawar cikin makara, kasancewar babu hanyar da mota za ta je garin.

Babban limamin garin Alhaji Lawal Liman Joɓawa, ya bayyana cewa hanyar ta haɗa ƙananan hukumomin Mani da Ɓatagarawa da Rimi, wadda idan aka gyara masu za ta inganta rayuwar al’ummar yankin.

Mai Unguwar garin Mamuda Bala da yake jawabi, ya ce suna yabawa kan kyakkyawan shugabancin Gwamna Dikko Umaru Raɗɗa, amma suna kira gare shi da ya kawo masu ɗauki kasancewar shi shugabane mai jin ƙan talakawa.

Shima Shugaban matasan garin Hamisu Sadi Joɓawa, ya ce suna kira ga Gwamna da ya yi masu ko da titin birji ne kafin wancan ya samu, domin sauƙaƙa masu na halin da suke ciki, da kuma bai wa motoci damar shiga garin, don rayuwar su da ta iyalan su.

Mai Unguwar garin Tarambi, ya bayyana cewa hanyar ta kasance ta fara daga garin Ajiwa ta biyo ta garin taje ta je Joɓawa ta isa Mani, inda yace idan aka gyara masu zai inganta rayuwar su da kuma tattalin arzikin yankin.

By ukarofi