*Kasashen Afirka na neman gyara yadda duniya ke kallonsu
Kasar Togo na shirin roƙon ƙasashen Majalisar ɗinkin Duniya su amince da sabuwar taswirar duniya da za ta nuna ainihin girman nahiyar Afirka, tare da watsi da tsohuwar taswirar Mercator.
Masu sukar Mercator sun ce tana nuna Greenland kamar tana da girman Afirka, alhali Afirka ta fi ta ninki 14 girma.
Kungiyar Tarayyar Afirka ta ɗora wa Togo alhakin jagorantar kamfen ɗin “Correct The Map” domin kawo ƙarshen amfani da wannan tsohuwar taswira.
Kamfen ɗin na kira da a rungumi taswirar Eƙual Earth ta 2018, wadda ke ƙoƙarin nuna ainihin girman ƙasashe ba tare da karkata ba.
Ministan harkokin wajen Togo, Robert Dussey, ya ce taswirar da ake amfani da ita yanzu ba ta da ingancin kimiyya.
Ya jaddada cewa wannan ba wai batun taswira kaɗai ba ne, har ma da yadda duniya ke kallon Afirka.
An riga an shirya ƙudirin doka da za a gabatar a Majalisar ɗinkin Duniya a watan Satumba.
Dussey ya ce yadda ƙasashe za su kaɗa kuri’a zai nuna ainihin matsayinsu kan Afirka.
A baya-bayan nan ma Majalisar ta amince da wani ƙudiri da ya bayyana bautar bayi a matsayin babban laifi, tare da kiran a biya diyya, amma wasu ƙasashe sun ƙi goyon baya.
