* Ya yi alƙawarin ƙarfafa haɗin gwiwa da Nijeriya
Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Shugaban ƙasar Amurka, Donald Trump, ya yaba wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan abin da ya bayyana a matsayin jajircewarsa wajen yaƙi da ta’addanci da magance matsalolin tsaro a Nijeriya, musamman hare-haren da ake kai wa al’ummomin Kiristoci.
Yabon na ƙunshe ne cikin wata wasiƙa mai ɗauke da kwanan watan 6 ga Yulin 2026, wadda Trump ya aikewa Tinubu, kuma Fadar Shugaban ƙasa ta fitar da ita ga manema labarai ranar Laraba ta bakin Mai Bai wa Shugaban ƙasa Shawara na Musamman kan Yaɗa Labarai da Dabaru, Bayo Onanuga.
A cewar sanarwar, Trump ya yaba da ƙoƙarin gwamnatin Tinubu na inganta tsaro, tare da sake jaddada aniyar Amurka na ci gaba da mara wa Nijeriya baya a yaƙin da take yi da ta’addanci.
A cikin wasiƙar mai taken “Trump ya yabawa Shugaba Tinubu kan ƙwazon jagorancinsa wajen yaƙi da ‘yan ta’adda,” shugaban na Amurka ya gode wa Tinubu bisa saƙon da ya aike masa, yana mai bayyana gamsuwarsa da yadda yake jagorantar Nijeriya wajen fuskantar ƙalubalen tsaro.
“Na gode da wasiƙarka mai cike da tunani. Kalamanka sun matuƙar birge ni, kuma ina yaba maka bisa jajircewarka wajen jagorantar al’ummar Nijeriya,” inji Trump.
Ya ƙara da cewa yana yabawa Tinubu saboda ƙudurin da ya nuna na kare al’ummomin da ke fuskantar hare-haren ‘yan ta’adda.
“Ina yabawa ƙudurinka na magance matsalolin da suka addabi ƙasarka, musamman hare-haren da ke shafar al’ummomin Kiristoci. Babbar daraja ce gare ni in kasance tare da kai a wannan yaƙi da ta’addanci domin ganin Nijeriya ta zama ƙasa mai ƙarfi da wadata,” inji shi.
Shugaban Amurkan ya bayyana cewa alaƙar da ke tsakanin Nijeriya da Amurka na ƙara ƙarfi, musamman a wannan lokaci da matsalolin tsaro ke ƙaruwa a yankin Afirka ta Yamma.
Ya ce ƙasashen biyu suna da buri guda na murƙushe ta’addanci a kowane irin salo, yana mai nuni da cewa Taswirar Haɗin Gwiwar Tsaro ta Amurka da Nijeriya ta 2026 (US-Nigeria 2026 Defence Cooperation Roadmap) ta samar da ingantaccen tsari na haɗin gwiwar tsaro tsakanin ƙasashen biyu.
“Dangantakar Amurka da Nijeriya tana da matuƙar muhimmanci a wannan lokaci da rikice-rikice suka bazu a Afirka ta Yamma da sauran sassan duniya. Muna da manufa guda ta yaƙi da ta’addanci a kowane irin salo, kuma taswirar haɗin gwiwar tsaro ta 2026 ta samar da ƙaƙƙarfan ginshiƙi domin cimma wannan buri,” inji Trump.
Trump ya kuma bayyana cewa Amurka ta tura rundunar ƙwararrun sojojinta na musamman domin taimaka wa Rundunar Sojin Nijeriya ta hanyar horaswa, musayar bayanan sirri da kuma bayar da goyon bayan ayyukan tsaro.
Ya ce matakin na da nufin ƙarfafa rundunar sojin Nijeriya wajen kare ƙasar, rusa sansanonin ‘yan ta’adda da kuma kare rayuka da dukiyoyin fararen hula, musamman al’ummomin da ke fama da hare-hare.
“Ina alfahari da tura rundunar ƙwararrun sojojinmu domin bai wa jaruman sojojin Nijeriya horo, kayan aiki da bayanan sirri da za su taimaka musu wajen kare ƙasarsu da tabbatar da tsaron jama’a,” inji shi.
Trump ya kuma bayyana fatan ci gaba da yin aiki kafaɗa da kafaɗa da Shugaba Tinubu a tsawon wa’adin mulkinsa.
Fadar Shugaban ƙasa ta ce Nijeriya da Amurka sun ƙara ƙarfafa haɗin gwiwarsu a fannin tsaro cikin ‘yan watannin nan, bayan kafa Kwamitin Haɗin Gwiwa da Mashawartan Tsaron ƙasa na ƙasashen biyu ke jagoranta.
Sanarwar ta ce haɗin gwiwar ya shafi horas da jami’an tsaro, musayar bayanan sirri, haɗa kai wajen gudanar da hare-haren tsaro da sauran matakan da za su raunana ƙungiyoyin ta’addanci da ke aiki a yankin.
Ta ƙara da cewa ɗaya daga cikin manyan nasarorin haɗin gwiwar shi ne farmakin haɗin gwiwa da aka kai ranar 16 ga Mayu a maboyar mayaƙan ISIS da ke yankin Tafkin Chadi, wanda aka ce ya yi sanadin kashe wani kwamandan ƙungiyar mai suna Abubakar Al-Minoki tare da wasu manyan jagororinta.
Haka kuma, Fadar Shugaban ƙasa ta bayyana cewa Mataimakin Sakataren Harkokin Wajen Amurka mai kula da Afirka, Frank Garcia, ya kai ziyara Abuja a makon da ya gabata, inda ya gana da manyan jami’an gwamnatin Nijeriya tare da sake tabbatar da aniyar Amurka na faɗaɗa haɗin gwiwa da Nijeriya a fannoni na tsaro, kariya da sauran muhimman sassa.
Sanarwar ta ce ƙasashen biyu sun kuduri aniyar ci gaba da faɗaɗa haɗin gwiwarsu domin tunkarar sabbin barazanar tsaro, inganta zaman lafiya a yankin da kuma ƙara wa hukumomin tsaron Nijeriya ƙarfi wajen yaƙi da ta’addanci da masu tsattsauran ra’ayi.
