Tsakanin Fulani da Bahaushe: InnalilLahi wa inna ilaihir rajiun!

Manhaja logo

Daga FATUHU MUSTAFA

Abinda masu wannan tunani suka dogara da shi na cusa wutar gaba tsakanin Hausawa da Fulani abu biyu ne, Jihadin Shehu da kuma ta’addancin da Fulani suke yi a yau. Musamman a Arewa maso Yamma na ƙasar nan.

Na yi iya ƙoƙari na in ga na kauce wa wannan shirme, amma na kasa daurewa, musamman da naga wani mutum da nake ganin ya girmi wannan shirmen Ahmad Musa Jingau ya yi wani rubutu da har yake cewa, ‘Fulani most be a pariah’. Wannan magana ta bani tsoro matuqa ƙwarai.

Domin kuwa ni ban ga yadda za ka iya tava raba bahillace da Bahaushe ba. Ba wani gida a Kano da walau dai bai da alakar auratayya tsakanin sa da Fulani, ko Hausawa ko Bare-bari. To wa za a mayar bare a ciki?

Bari in sanar da mutane su sani, Hausawa ne tushen jihadin Shehu Usman ba Fulani ba. Domin da farko dai, kusan manyan malaman sa da yake ji da su, wadanda suka daura shi a kan hanya kusan a iya cewa Hausawa ne, musamman babban malaminsa, Jibril Ghaini Bagobiri da Hashim al Bazamfari, kamar yadda Shehu Abdullahi ya kawo a Idha’un Nusk.

Babban abinda ya janyo jihadi ba ƙabilanci ba ne, abu biyu ne, zalunci da ya yi katutu a tsakanin sarakunan ƙasar Hausa, da kuma rauni da koyarwar addini da tarbiyya suka yi, domin ka tabbatar da haka, ka nemi Shurb al Zulal in da aka baje kolin irin halayen ni ‘ya su da ƙasar Hausa take ciki kafin jihadi.

Wani abin lura, wasiqar Sarkin Yunfa zuwa ga Sarakunan ƙasar Hausa, ita ta fara mayar da jihadin ya zama kamar na Fulani ne da Hausawa. To amma a lura, ba dukkanin Bahaushe ne ya goya wa sarakunan Hausa baya ba, domin irin su ƙadhi Usmanul Hausawi a Kano, da su Malam Yakubu a Bauchi da Sarkin Zazzau Jatau da irin su Malam Umaru na Na Alhaji a Katsina, kai har ma da Sarkin Katsina Muhammadu Gozo, da su Sarkin Zamfara Abarshi, Galadiman Sakkwato Doshero, da irin su Chiroman Kano Ɗanmama da wasu da dama dukkan su Hausawa ne kuma jigogi ne a jihadin Shehu.

Ko shakka ba na yi da Sarkin Katsina Gozo ya rayu har lokacin Jihadi da da shi za a mara wa Shehu baya. Ga kuma Bare-bari irin su Sarkin Zazzau Yamusa, Malam Ibrahim al Barnawi wanda a yanzu zuriyar sa ke rike da Shettiman Damagaram. Waɗannan kaɗan ne daga Hausawa na usul da suka dafa wa jihadin Shehu.

Haka ma akwai Fulani da dama da suka nuna ƙyamarsu ga jihadin Shehu, abin mamakin ma har a cikin gidansu, domin yayansa Malam Ali bai tava yadda da jihadin Shehu har ya bar duniya. Haka ma Sarkin Fulanin Ingawa ya fito ƙarara ya yaƙi Fulani yan’uwansa a lokacin da suke neman taimakonsa, wannan dalili ne ya haddasa wutar gaba tsakaninsa da Sarkin Kazaure Ɗantunku, har sai da daga baya Umar Dallaji ya shiga tsakani.

Haka ma ko a Kano ba dukkan Fulani ne suka amince da Jihadin ba, akwai ƙabilun Fulani da dama da suke ganin kawai jihadin wani nau’i ne tayar da fitina a cikin mutane.

Don haka, ni a ganina zancen a ce jihadin Fulani bai taso ba, domin ba Fulani ne zalla suka taru suka yi jihadi ba, sai dai kawai Fulani ne mafiya akasarin waɗanda suka yi jihadin. Amma akwai Hausawa da dama da suka mara musu baya, kuma suka zama jigajigai a lokacin gwagwarmayar.

Ya kamata a fahimta cewa, maƙasudin fito na fito da Shehu ya yi da Sarakunan Gobir ba saboda takurawar da aka yi masa ba ne ko kuma ƙabilarsa ta Fulani. Dokar da Sarakunan Gobir irin Bawa Jangwarzo da Wurno Nafata da su Yunfa suka kafa ta shafi duk wani malami ne ko kuma dukkan wani musulmi da ke bi, ko yake salon wa’azi irin na Shehu.

Babu inda dokar ta ce Fulani kawai ta shafa. Malaman Hausawa da dama sun shiga fursun saboda biyayyar su ga Shehu. Ya kamata a sani, ɗaya daga cikin sharuddan da Shehu ya kafa wa Sarakunan Gobir sun haɗa har da, a saki Sarkin Zamfara Abarshi, wanda kowa ya san cikakken Bahaushe ne, da tun zamanin Bawa aka mayar da shi fursunan yaki.

Wanda Shehu ke ganin zalunci ne, bayan an ƙwace masa gari, wato Sabon Birni, an kuma kashe iyayensa da kakanninsa da yan’uwansa, an kuma kama shi a saka a kukumi.

Ina ganin ya kuma kamata a sani, babban wanda ya janyo aka ɗau makami aka fafata ba fa bahillace ba ne, bahaushe ne, bagobiri kuma, wato Malam Abdussalami, wanda shi ne farkon wanda ya fara fito na fito da sarakunan Gobir, kuma a kan wannan ya sanya ya yi hijira wurin Shehu ya kai caffa. Yunfa ya nemi Shehu da ya bayar da shi, domin a yi masa hukunci amma Shehu ya qi, dalilin da ya sanya mai aukuwa ta auku a tsakaninsu, har aka fara jihadin a bakin Tafkin Kwatto.

Da wannan nake cewa, ya kamata duk wasu masu hankali su tashi tsaye su yaqi wannan babban bala’i da ya taso mana, ya kamata manya su tashi tsaye su kashe wannan wuta tun ba ta kama yayi ba. Abinda ya faru a tsakanin Tutsi da hutu a Rwanda da abinda ya faru na Holocaust a yakin duniya na 2 ya ishe mu ishara.

Ba za ka tava raba bahaushe da bahillace ko babarbare ba, zama ne Allah ya haɗa mu tun shekaru aru-aru. Mu sani, ko da ƙabila ta raba mu, amma ai addini ya haɗa mu. Haka kuma shi ɗan fashin daji, bai san waye bahillace ko bahaushe ba, duk wata magana da suke ta cewa wai suna yi ne don wasu haƙƙoƙinsu, ƙarya ne, ai sun san waɗanda suka danne haƙƙoƙin nasu, me ya haɗa talakawan da suke kamawa suna zalunta da azzaliman da suka hana su haƙƙin nasu?

Idan kunne ya ji, jiki ya tsira. Abinda duk zaman lafiya bai kawo ba, wallahi tashin hankali ba zai kawo ba. Allah ya ba mu lafiya da zaman lafiya! Amin!

Fatuhu marubuci ne, mai sharhi a kan al’amuran yau da kullum. Ya rubuto daga Kano.