Tuna baya: Sheikh Ja’afar ya cika shekara 16 da rasuwa

Daga NASIR S. GWANGWAZO a Abuja

A jiya Alhamis, 13 ga Afrilu, 2023, shahararren malamin addinin Islama, Marigayi Sheikh Ja’afar Mahmud Adam ya cika shekara 16 da rasuwa.

Malam Ja’afar, kamar yada wasu ke kiran sa, ya rasu ne sakamakon harbin binidga a masallacinsa dake gadon unguwar Ɗorayi a birnin Kano yayin da ya ke limancin sallar Asuba ta ranar Juma’a, 16 ga Afrilu, 2007.

Shafin Wikipedia ya ruwaito cewa, an haifi Malam Ja’afar a ranar 12 ga, Fabrairu, 1960, kuma ya bar duniya 13 ga Afrilu, 2007. Haifaffen garin Daura ne ta Jihar Katsina, amma ya girma a birnin Kano. Ya rasu ne sanadiyar harbin bindiga daga wasu da ba a san ko su wane ne ba, inda sun harbe shi ne a lokacin da yake sallar Asubahi a masallaci a garin birnin Kano a Unguwar Ɗorayi.

Malamin addinin Musulunci ne, Ahlus-Sunnah, ma’ana: mabiyin ƙungiyar Jama’atu Izalatul Bid’ah Wa Ikamatus Sunnah Izala ne a Nijeriya, ƙungiyar addinin Musulunci da take ƙoƙarin kawar da Bidi’a (wato ibadun da ba su da tushe a Musulunci) da tabbatar da Sunna ta Ma’aiki Manzon Allah SAW, wanda babbar cibiyar ƙungiyar ta ke a garin Jos.

Bayan haka ya kasance mallamin tafsirin Alƙur’ani mai girma, sannan za a iya cewa shi ne jagoran Salafawa-Sunni a Nijeriya.

Sheikh Ja’afar, wanda ya hardace Alƙur’ani a shekara ta 1978, yana yin wa’azin tafsirin Ƙur’ani a Masallacin Indimi a birnin Maiduguri, Babban Birnin Jihar Borno, wanda yake samun halartar Mataimakin Gwamnan Jihar Borno a wancan lokaci.

An kashe Sheikh Adam ne a masallacinsa da ke unguwar Ɗorayi cikin birnin Kano, wacce ta ke Arewacin Nijeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *