Tinubu a kotu: Atiku ya saba shan kayin zaɓe

Spread the love

*Ya roƙi ga ɗan takarar na PDP
*Dalilan da suka hana Atiku cin zaɓe, inji Tinubu

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasa mai jiran gado, Bola Ahmed Tinubu, ya ce, ɗan takarar Shugaban Ƙasa na Jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, a kodayaushe yana shan kayi a yunƙurinsa na neman shugabancin Nijeriya tun shekarar 1993.

Don haka sai Tinubu ya roqi Atiku da kada ya kalli rashin nasararsa a zaɓen da ya gabata a matsayin baƙon abu, yana mai cewa, hakan ba zai zama abin al’ajabi ga Jam’iyyar PDP da ɗan takararta idan aka yi la’akari da rikicin da ya dabaibaye jam’iyyar kafin zaɓe da kuma lokacin zaɓe.

Zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasar ya bayyana haka ne a martanin da ya mayar kan ƙarar da Atiku da PDP suka shigar a gaban Kotun Sauraron Ƙararrakin Zaben Shugaban Ƙasa, inda suke roƙon a bayyana shi a matsayin wanda ya yi nasara ko kuma kotu ta bayar da umarnin a sake zaɓen.

Ya ƙara da cewa, Atiku ba shi da tsayayyen tsarin siyasa, kuma ya yi asarar mafi yawan manyan magoya bayansa, duba da yadda yake tsalle daga wannan jam’iyya zuwa waccan.

Tinubu ya kuma bayyana cewa, fitowar Atiku a matsayin ɗan takarar PDP ne ya ƙara ruruta wutar rikicin da ta ke faruwa a jam’iyyar, wanda ya sa gwamnoninta guda biyar suka yanke shawarar yi masa qafar ungulu tare da tabbatar da cewa ya sha kayi.

Tawagar lauyoyinsa ƙarƙashin jagorancin Wole Olanipekun ne suka shigar da martanin zaɓen Shugaban Ƙasa.

Zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasar ya bayyana ƙarar a matsayin ba kawai a banza ba, amma cin zarafin tsarin kotu.

Ya ce tun da farko PDP ta shigar da ƙara a Kotun Ƙoli, ta hannun wasu gwamnoninta, inda ta buƙaci a soke zaɓen, ba za ta iya ci gaba da shari’o’i biyu kan batu guda a kotuna daban-daban a lokaci guda ba.

Ya bayyana cewa, a ranar 28 ga watan Fabrairu, Jam’iyyar PDP ta hannun gwamnoninta na jihohin Adamawa, Akwa-Ibom, Bayelsa, Delta, Edo da Sakkwato sun shigar da ƙara a Kotun Ƙoli, inda suka buƙaci da a soke zaɓen Shugaban Ƙasa da aka yi a ranar 25 ga watan Fabrairu.

Ya kuma nuna rashin amincewa da cancantar ƙarar a kan cewa an cire Peter Obi na jam’iyyar Labour Party (LP) da Rabiu kwankwaso na Jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) duk da cewa masu shigar da ƙara sun fafata da sakamakon zaɓen jihohin da suka samu nasara, LP da NNPP.

Masu shigar da ƙara sun koka kan sakamakon zaɓen da aka gudanar a jihohin Abia, Anambra, Delta, Ebonyi, Edo, Enugu, Imo, Kano, Filato da Legas, kuma ba a bayyana Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaɓen gaba ɗaya ba a jihohin.

Martanin da tawagar Tinubu ta bayar ya qare ne da tambaya kan koken Atiku kan sakamakon zave a dukkan jihohin da shi Obi ya lashe zaɓen da suka haɗa da Adamawa, Bauchi, Akwa-Ibom, Bayelsa, Gombe, Yobe, Sakkwato. Jihohin Osun, Kebbi da Katsina, ba tare da sun mayar da kansu masu amsa wannan buƙata ba; yayin da a ƙarƙashin sashe na 133 (2) na Dokar Zaɓe, 2022, jam’iyyar da ake ƙalubalantar zaɓenta za ta zama mai amsa tambayoyi.

By Editor